Sadarwa: Amfani da Ido

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sadarwa: Amfani da Ido


Gabatarwa

Bahaushe yana amfani da ido wajen bayyana soyayya, shagwaɓa, dakatarwa, da sauransu.

  1. Farfari: Farfari, hanyar sadarwa ce ta gargajiyar Bahaushe, wacce yake nuna soyayya da shi. Mata, su suka keɓanta da nuna soyayya ga maza ta hanyar farfari. Idan mace ta yi farfari tare da ɗan murmushi, to wannan soyayya ce. Idan kuma ta yi farfari tare da zumɓura baki, wannan na iya zama na raini. Idan kuma yaro ne ya yi, to wannan shagwaɓa ce. Ana yin farfari ta hanyar rufe idanuwa biyu sannan kuma a buɗe su da-sauri-da-sauri a tare.
  2. Ƙifce: Alama ce ta jan hankali ko kuma dakatarwa. Idan mutum yana cikin magana a muhallin da ba damar a ce da shi bari, sai a ƙifta masa ido sau ɗaya domin dakatar da shi daga cigaba da wannan zance da yake yi.
  3. Mafi yawancin lokaci, ana dakatar da mutum daga zance ta hanyar ƙifce idan ya zama yana faɗin maganar da bata dace ba game da wani mutum sai kuma ya zama shi mutumin ko wani nasa ya bayyana a wajen ba tare da sanin mai maganar ba, ko ma idan aka tsinkayo wani makusancin wanda ake maganar a kansa yana dosowa, to sai a ƙiftawa mai magana ido domin ya dakata da maganar.

    Shi kuwa ƙifce ana yinsa ne ta hanyar rufe idanuwa biyu a buɗe sau ɗaya a hankali.

  4. Kanne: Kanne shi ne a rufe ido ɗaya sannan a buɗe shi da sauri-da-sauri tare kuma da ɗan karkatar da kai ta gefen idon da aka yi kannen da shi. Ana yin kanne domin ankararwa.
  5.  Zare Ido: Bahaushe kan zaro idanuwansa gwala-gwala ko dara-dara domin nuna halin tsoro musamman lokacin da ya yi arba da wani abin tsoro kamar wata dabba da sauransu.
  6. Linshe Ido: Bahaushe na nuna kunya da kuma ƙasƙantar da kai ta hanyar linshe idanu, sannan a sunkuyar da kai ƙasa. Shi linshe ido shi ne rufe idanu amma ba rif ba. Sannan kuma a wasu lokutan linshe idon na nuna alamun barci. Shi kuwa linshe idanun barci ana gane shi ne idan ya zama mutum ya linshe idanun sannan yana yin ɗan layi ko kuma yana magana yana katsewa ko kuma yana hamma.
  7. Rintse Ido: Bahaushe yana rintse idanunsa domin nuna tausayi. Shi kuma rintse ido shi ne mutum ya rufe idanuwansa da bakinsa a lokaci guda tare da yamutse fuska. Misali, idan Bahaushe ya ga ana tsattsaga jikin yaro, yakan rintse idanuwansa da nufi cewa baya son ganin zubar jinin da kuma kukan da yaron yake yi.

Manazarta:


Bunza A.M. (2002). Rubutun Hausa Yadda Yake Da Yadda Ake Yin Sa Don Masu Koyo Da Koyarwa. Ibrash Islamic Publications Centre L.T.D., 31 Adalabu Street, Surulere, Lagos.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A.A. da Alhassan B.S.Y. (2011). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire Littafi na Ɗaya. University Press PLC, Ibadan, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub