Sadarwa: Amfani da Kai

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sadarwa: Amfani da Kai


Gabatarwa

Idan muka ɗauki kai ɗungurungum daga wuya zuwa abin da ya yi sama, za mu taras cewa, ya haɗiye sassan da suka haɗa da fuska, ido, hanci, baki da kuma kunnuwa.

Gundarin Kai

Bahaushe yana amfani da gundarin kansa ɗungurumgum wajen:

  1. Amincewa: Bahaushe yana nuna amincewa da abu ta hanyar gyaɗa kai. Shi kuwa gyaɗa kai shi ne a ɗaga kai sama sannan a dawo da shi ƙasa cikin ruwan sanyi sannan a ɗan girgiza shi (ya yi sama ya dawo ƙasa kamar sau biyu). Yin wannan daidai yake da faɗin “To” ko kuma “E” da baki.
  2. Ƙin Amincewa: Bahaushe yana nuna rashin amincewa da abu ta hanyar kaɗa kaɗai. Shi kuwa kaɗa kai ana yin sa ne ta hanyar juya kai daga dama zuwa hagu ko kuma daga hagu zuwa dama, duk ta gefen da aka fara daidai ne. Yin haka daidai yake da faɗin “A’a” ko kuma “Ban yarda ba”.
  3. Tsawatarwa: Bahaushe yana tsawatarwa ta hanyar kaɗa kai da sauri-da-sauri fiye dana  ƙin amincewa sanan kuma a halin fuska tana murtuke. Yin wannan, daidai yake da faɗin “Kai” ko “Kul” ko “Bari” da sauransu.

Manazarta:


Bunza A.M. (2002). Rubutun Hausa Yadda Yake Da Yadda Ake Yin Sa Don Masu Koyo Da Koyarwa. Ibrash Islamic Publications Centre L.T.D., 31 Adalabu Street, Surulere, Lagos.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A.A. da Alhassan B.S.Y. (2011). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire Littafi na Ɗaya. University Press PLC, Ibadan, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub