Sadarwa: Saƙon Kar-Ta-Kwana

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sadarwa: Saƙon Kar-Ta-Kwana


Gabatarwa

Kalmar kar-ta-kwana, kalma ce da aka samar da ita daga kalmomi uku; kar da ta da kuma kwana, wacce idan aka fassara ta, za ta iya ɗaukar ma’ana ta, “kar wasiƙar ta kwana”. Hanya ce ta isar da saƙon gaugawa a gargajiyance.

Ana aika wannan saƙo ta hanyar tanadar dawakai a garuruwan da ke kan hanyar da saƙon zai bi kafin ya isa asalin garin da ake son ya je. Misali, idan saƙon zai tashi daga garin farko zuwa garin da ake son ya je wanda shi ne gari na ƙarshe, to za a tanadi dawakai a wasu garuruwan da tazarar da ba za ta gajiyar da dawakan ba. Da zarar ɗan saƙon farko ya karɓi saƙon, sai ya zaburi dokinsa da gudu, ba tsayawa sai ya kai gari na farko. Kenan, da shi da dokin duk za su isa garin a gajiye. Daga nan zai damƙa saƙon a hannun mutum na biyu, shi ya runtuma da gudu zuwa gari na gaba. Da haka-da-haka har saƙon ya je garin da ake so. Hikimar hakan ita ce ƙara saurin kai saƙon da kuma samawa dawakai da masu kai saƙon sauƙi.

Manazarta:


Bunza A.M. (2002). Rubutun Hausa Yadda Yake Da Yadda Ake Yin Sa Don Masu Koyo Da Koyarwa. Ibrash Islamic Publications Centre L.T.D., 31 Adalabu Street, Surulere, Lagos.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A.A. da Alhassan B.S.Y. (2011). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire Littafi na Ɗaya. University Press PLC, Ibadan, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub