Sadarwa: Kayan Kiɗa

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sadarwa: Kayan Kiɗa


Gabatarwa

Bahaushe yana amfani da kayan kiɗa na gargajiya wajen isar da saƙonni. Daga ciki akwai:

Busa Ƙaho

Ana busa ƙaho domin sanar da mazaje su yi shirin fita daji domin farauta.

Ganga

Ana kaɗa ganga domin sanar da yin wasanni kamar irin su kokawa da saurnsu. Misali, idan za a yi wasan kokawa, to mai ganga yakan yi ta kaɗawa na tsawon lokaci domin sanar da mutane cewa, an fara taruwa. Wannan ita za ta saka mutane su yi ta fitowa zuwa gurin da suke jin wannan amon.


Gangar Kokawa

Sarewa

Samari kan busa wa ‘yan matansu sarewa domin sanar da su cewa su fito zance.

Kurya

Kurya ganga ce da ake kaɗa ta a lokacin da ake son sanar da jama’ar gari cewa su yi shirin fita yaƙi a lokacin yaƙe-yaƙe.

Kuge

Wasu ƙarafuna ne na kiɗa da ake buga su da juna. Ana amfani da su wajen sanar da mazaje fita yaƙi.

Bindiga

Ana harba bindiga domin sanar da jama’a ganin watan azumi ko na sallah. Sannan kuma idan aka idar da sallar Juma’a a babban masallaci akan harba bindiga domin sanar da matan da ke cikin gida cewa an sauko daga Juma’a domin suma su shirya su yi sallar azahar.

Manazarta:


Bunza A.M. (2002). Rubutun Hausa Yadda Yake Da Yadda Ake Yin Sa Don Masu Koyo Da Koyarwa. Ibrash Islamic Publications Centre L.T.D., 31 Adalabu Street, Surulere, Lagos.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A.A. da Alhassan B.S.Y. (2011). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire Littafi na Ɗaya. University Press PLC, Ibadan, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub