Sadarwa: Amfani da Sauti

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sadarwa: Amfani da Sauti


Gabatarwa

Bahaushe yana amfani da sauti wajen sadarwa. Sauti kuwa a nan yana nufin amo wanda ka iya zama na murya ko waninta. Daga ciki akwai:

Shela/Yekuwa

A gargajiyance, shela/yekuwa, hanya ce ta isar da saƙo daga mai gari/sarki zuwa ga talakawa. Ta wannan hanya ake sanar da jama’a wani saƙo da sarki yake son su sani. Shugaban maroƙa; wato sanƙira kenan, shi yake yin shela. Yakan ce, “Yeeeeekuwa jama’ar gari, sarki ya gaishe ku, ya kuma ya gaishe ku, ya ce a sanar da ku cewa, gobe idan Allah ya kai mu, akwai noman gandun sarki”.

Guɗa

Ƙara ce mai ƙarfi da ake fitar da ita ta hanyar baki da hanci. Mata ne suke yin guɗa domin sanar da haihuwa ko kuma wani abin farin ciki da ya faru a gida. Ana yin guɗa ta hanyar matse hanci a rufe shi da yatsu sannan a lanƙwasa harshe ana karkaɗa shi sai kuma a turo iska daga maƙogwaro.

Ihu

Ihu alama ce da Bahaushe ke amfani da ita wajen nuna shiga halin damuwa tare kuma da neman agaji. Haka nan kuma idan ana aikin gayya ko a gida ko a gona, akan kwarma ihu.

Kururuwa

Kururuwa ihu ce na mutane masu yawa a lokaci guda. Ana yin kururuwa domin neman agajin gaugawa a lokacin da aka tashi ɓarawo ko kuma a halin gobara.

Kuka

Kuka hanya ce ta sanar da ɓacin rai ko shiga wani mummunan hali ko wata damuwa da tafi ƙarfin juriyar mutum.

Sowa

Sowa ita ce kuka haɗe da ihu; wato mutum yana kuka da ƙarfi. Alama ce ta nuna matsananciyar damuwa ko tashin hankali.

Manazarta:


Bunza A.M. (2002). Rubutun Hausa Yadda Yake Da Yadda Ake Yin Sa Don Masu Koyo Da Koyarwa. Ibrash Islamic Publications Centre L.T.D., 31 Adalabu Street, Surulere, Lagos.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A.A. da Alhassan B.S.Y. (2011). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire Littafi na Ɗaya. University Press PLC, Ibadan, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub