Hausa Wasan Shaɗi

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Wasan Shaɗi


Gabatarwa


Taron Shaɗi

Wasan shaɗi yana ɗaya daga cikin bukukuwan Ƙasar Hausa. Wasa ne da Fulani ke yin sa. Babbar manufar wannan wasa ita ce nuna jarumtaka. Fulani suna ganin saurayin da bai yi shaɗi ba a matsayin rago.

Ana yin shaɗi ne ta hanyar duka da bulalar da sai dabbobi kamar jakai da makamantansu za a iya duka da ita su zauna lafiya. Matashi Bafulatani zai cire rigarsa, sai ya zauna ko a kan turmi, ko ya dogara ƙafa ɗaya a kan wani, da makamantansu. Sai abokin shaɗinsa ya samo bulala (suna yawan amfani da bulalar icen tsamiya) ya riƙa zumbuɗa masa, shi kuma yana tsaye ko gezau ba zai yi ba. Idan ya jure wannan bulala zuwa adadin da ya ɗauka; wasu sukan ɗauki biyu har zuwa goma sha biyu, wasu ma har fiye, to sukan samu kwarjini a wajen maza sannan kuma su samu farin jini a wajen mata fulani 'yan'uwansu.

Shaɗi

Manazarta:


Barau A. S. (2007). The Great Attraction of Kano State. Research and Documentation Directorate, Office of the Executive Governor, Government House, Kano.

Masarautar Dutse (2015). Festivals and Ceremonies in Dutse Emirate. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: www.dutseemirate.com

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A. A. da Alhassan B.S.Y. (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire, Littafi na Uku. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Darrusan Hausa

 • Darrusan Hausa

 • Bukukuwa


  Wasanni  Ƙasar Hausa  Musulunci


  Zuwan Turawa


  Tarbiyya


  Kayan Kiɗan Hausa


  Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


  Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin  Sauran Shafukanmu:

  Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub