Tatsuniya
Gabatarwa
Tatsuniya, ƙagaggun labarai ne na ƙarya waɗanda babu ƙanshin gaskiya a cikinsu, waɗanda Hausawa kan shirya don annashuwa da hira (Junaidu da ‘Yaraduwa, 2002).Rabe-Raben Tatsuniya
Tatsuniya iri biyu ce:- Tatsuniya ta Kacici-kacici: Ita wannan tatsuniya, tana ƙunsar tambaya ne da amsarta. Amsar tambayar, sau da yawa tana yin kama da tambayar, dangane da sauti da ma’ana (Ɗangambo, 1984).
- Tatsuniya mai labari: Tatsuniya mai labari ita sauraro kawai ake yi ba a ba da amsa. Misali, tatsuniyoyin da suka ƙunshi su Gizo, Ƙoƙi, Dodo, Kura, Zaki, Damo, Giwa, ‘Yar Bora da ‘Yar Mowa, da sauransu da yawa. Cikin irin waɗannan tatsuniyoyi, akan sami mutane, dabbobi da sauransu. Akan kuma nuna yadda dabbobi da dodanni ke magana ko hulɗa da mutane da sauransu.
Tatsuniya ana yin ta ne da daddare. Tsofaffi da manya, sukan tara yara, suna yi musu tatsuniya, su kuma koya musu cewa, su ma yaran, su riƙa yin tatsuniya (Ɗangambo, 1984).
Manazarta:
Ɗangambo A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Maɗaba’ar Kamfanin ‘Triumph’, Gidan Sa’adu Zungur, Kano.
Junaidu I. da ‘Yar’aduwa T.M. (2003). Harshe da Adabin Hausa a Dunƙule don Manyan Makarantun Sakandire. Spectrum Books Limited.
Zube
Zube
Tatsuniyoyi
- Gizo da Noman Gyaɗa
- Gizo da Saniya
- Gizo da Ƙoƙi da Kantu
- Gizo da Ɗanrago...
- Gizo Ɓarawon Gyaɗa
- Gizo da Ɓaure
- Biri da Kura
- Kura da Kare
- Auren Barewa...
- Kuturu, Makaho...
- Alhaji da Hajiya
- Wasu Mutane Huɗu
- Baban Rogaji
- Yarinya da Ƙawayenta
- Mutum da Zabi
- Ƙuda da Kwaɗo
- Ɓarayin Rake
- Maraya
- Ɓarawon Gwal
- Tsiniyama da Lafiyana
- Yusufu da Bala
Bukukuwa
Wasanni
Karin Magana
Wakokin Makaɗa
- Waƙoƙin Makaɗa
- Makaɗan Fada
- Makaɗan Sarauta
- Makaɗan Jama’a
- Makaɗan Maza
- Makaɗan Mata
- Makaɗan Ban-Dariya
- Makaɗan Sana’a
Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:
TweetLatsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin