Zube

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Zube


Gabatarwa

Zube, reshe ne na Adabin Baka ko Adabin Gargajiya, wanda kuma zantuttuka ne na hikima da ake shirya su da nufin koyar da dabarun zamantakewa ta cikin sigogi da dama. Waɗannan zantuttuka sukan zama gajeru ne ba masu tsawo ba, sannan kuma da ka ake shirya su; wato ta salon nan da ake cewa kara-zube. Shi ne dalilin da ya saka aka cire kalmar karan aka ɗauki zube aka yi mafani da ita wajen bashi suna.

Salon yadda aka tsara zancen, shi ke bambanta shi da saura. Saboda haka zube, yana da rassa da suka haɗa da:

Manazarta:


Ɗangambo A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Maɗaba’ar Kamfanin ‘Triumph’, Gidan Sa’adu Zungur, Kano – Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M. da ‘Yar’aduwa T.M (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire, Littafi na Uku. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A. A. da Alhassan B.S.Y. (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire, Littafi na Biyu. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub