Attah Arudi Ƙasar Ibira

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Attah Arudi Odano 1917 A.D.


Gabatarwa

Bayan rasuwar Attah Omadivi, sai kuma Turawa suka sake naɗa Attah Arudi Odano a matsayin sabon babban sarkin Ƙasar Ibira wanda shima ya mutu bayan wasu ‘yan watanni da naɗin nasa.

Wannan rasuwa ta sabon sarkin ƙasar Ibira ta buɗe sabon shafin fafutikar neman wannan kujera daga ɓangaren shahararrun mutanen wannan yanki. Sannan kuma suma ta nasu ɓangaren Turawan suna laluben mutumin da suke ganin shi ne mafi dacewa su marawa baya idan ya ɗare wannan kujera ta shugabancin ƙasar Ibira.

Ta ɓangaren Sir Frederick Lugard kuma shi ya fi son a samu nagartaccen mutumin da za su yi amfani da shi wajen mulkar jama’a a fakaice wanda shi ne zai zama shugaban hukumar gargajiya (native authority).

A cikin irin wannan hali su Turawa suka zaɓi Onoruoiza Ibrahim. Waɗanda suka nemi wannan sarauta tare da shi Onoruiza Ibrahim akwai Ozigizigi, Owada Adidi da kuma sauran jama’a masu yawa.

Manazarta:


Edo V. O. (2008). The Evolution and Development of Central Administration in Ebiraland, 1920-1997. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://www.nobleworld.biz/images/Edo.pdf

Okene A.A. da Suberu O.A. (2013). The British Conquest of Ebiraland, North Central Nigeria 1886-1917: A Military Interpretation of Sources. Professor (History & International Studies) Nigerian Defence Academy Kaduna, Africa’s Top Military University PMB 2109, Kaduna – Nigeria. American International Journal of Contemporary Research Vol. 3 No. 6; June 2013.

Segun J. A. (2013). Politics and Conflicts: A Study Of Ebiraland, Nigeria (1977-2007). Department of Political Science and International Relations, School of Social Sciences, College of Development Studies, Covenant University, Ota, Nigeria.Masarautar Okene

Sarakuna Ƙasar Ibira

Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafinSauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub