Attah Ibrahim Ƙasar Ibira

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Attah Ibrahim 1917 - 1954 A.D.



Fadar Attah Ibrahim ta farko
Tana kan Dutse a Okene.


Gabatarwa

Attah Ibrahim shi ne sarkin ƙasar Ibira na uku wanda Turawa suka naɗa. Kuma shi ne ya zama sarki na farko da ya fara jagorantar hukumar gargajiya (native authority). Naɗinsa ya biyo bayan gajeren wa’adin mulkin da sarki Arudi Odano (1917) ya yi. Attah Ibrahim jika ne ga Attah Omadivi (1904 -1917) ta ɓangaren mahaifiyarsa; wato mahaifiyar Attah Ibrahim 'ya ce ga Attah Omadivi (1904 -1917). Sarki Attah Ibrahim ya mulki ƙasar Ibira tsawon shekaru talatin da bakwai. Duk da turjiya da ya samu daga ‘yan’uwansa Ibira da kuma matsin lamba daga Turawa wanda hakan ta sabauta masa murabus. Mulkinsa ya mamaye dukkan ƙasar Ibira sannan kuma ya tsallaka zuwa yankunan Lokoja, Ogori da Magongo.

Haihuwa

Attah Ibrahim ɗa ne ga Zainabu wacce aka fi sani da Iy’ebe. Wannan mata sananniya ce sosai a ƙasar Ibira, ta yi fice wajen kasuwanci. Ita kuma ‘ya ce ga Attah Omadivi. Wato kenan shi Attah Ibrahim jika ne ga Atta Omadivi. Haka nan shi jikan jika ne na Ohindase Abogunde, wanda shi ne babban shugaban Unuguwar Okengwe.


Fadar Attah Ibrahim ta biyu.
Wannan fanfo an samar da shi tun 1938

Karatu

Kasancewar Attah Ibrahim Musulmi, ya fara tasowa da karatun addinin Musulunci inda ya fara karatun nasa a hannun babban malami Malam Abdul Salami na Ilorin. Daga baya kuma ya tafi garin Bidda dan samun karatu mai zurfi. Attah Ibrahim yana magana da yarurrukan Hausa, Nupe, Larabci da kuma Turanci.

Gogayyar Aiki

Tun cikin shekarar 1908 zuwa 1911 Attah Ibrahim yake aiki da Turawa a matsayin tafinta (mai fassara maganar Turawa zuwa ga ‘yan’uwansa Ibira, sannan kuma ya fassara maganar Ibira zuwa ga Turawa) musamman F.F.W. Byng-Hall.

A shekarar 1917 ya zamo marubucin F.F.W. Byng-Hall ta fuskar haraji. Turawan sun yi matuƙar jin daɗi da aikin da Attah Ibrahim yake musu a wancan lokacin, har ta kai ga shi F.F.W. Byng-Hall ya yabe shi ya ce, “Na same shi mai matuƙar amfani wajen hulɗa da Ibira” (Edo, 2013).

Zamowarsa Sarki

An naɗa Attah Ibrahim a matsayin sarkin dukkan ƙasar Ibira a shekarar 1917. Kuma shi ne mai kula babbar kotun Ebira mai daraja ta biyu (Grade B Court), sannan kuma shi ne babban jami’in hukumar gargajiya (native authority) ta ƙasar Ibira.

A iya tsawon mulkinsa na shekaru 37, shi ne ya mulki lardi mafi faɗi a dukkan arewacin Najeriya. Ya kuma kafa tarihin zamowa mutumin farko da ya fara mulkar dukkan ƙasar Ibira da kuma wasu yankuna da a yanzu suke cikin ƙasar Igala Lokoja, Ogori da Magongo a lokaci guda.

Gudunmawar da ya Bayar

Duk da matsin-lamba da ya samu daga jama'ar Ibira, Attah Ibrahim ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen kawo ci gaba ta fuskar haɓɓakar harkar Ilimi da sauran abubuwa a wannan ƙasa ta Ibira. Daga cikin abubuwan da suka samu a zamanin mulkinsa akwai samar da ruwan sha a Okene, hukumar Masarautar Okene, babban masallacin Okene, gina tituna a garin na Okene, makarantar tsakiya (Middle School) ta Okene, asibitin 'yan-mishan ɗin Sudan na Okene, fas ofis (post office) na Okene, da sauran abubuwa masu tarin yawa waɗanda ake ganin tun barinsa karagar mulki a shekarar 1954 kaɗan ne suka ƙaru wasu kuma ma an bar su sun lalace (Edo, 2013).

A taƙaice ma dai ana ganin cewa shi ne wanda ya kafa tubulin samuwar haɗin kan wannan yanki da a yau ake ƙira ƙasar Ibira. Shekaru da dama manazarta suna ganin cewa ba a taɓuka wani abun a-zo-a-gani ba tun bayan barinsa gadon sarauta, a maimakon haka ma an bar wasu ne sun rushe musamman cibiyar samar da ruwan sha ta Okene (Edo, 2013).

Barinsa Mulki

Duk da irin biyayya da Attah Ibrahim yake yiwa Turawa, ba za a rasa tangarɗa a tsakaninsu ba. Hausawa suna cewa tsakanin harshe da haƙori ma ana saɓawa. Saboda haka akwai rashin jituwa tsakanin Attah Ibrahim da wasu daga cikin Turawa musamman Sharwood Smith wanda yake a matsayin gwamnan arewa na wannan lokacin. A saboda haka su Turawa suna yi masa ganin mai yiwa mulkinsu zagon ƙasa alhali kuma su suka naɗa shi.

Haka nan a ta ɗaya ɓangaren kuma jama’arsa wato Ibira, suna yi masa kallon wanda ya kankame komai a hukumar gargajiya, saboda guguwar sauyin Dimokuraɗiyya da ke filfilawa a wancan lokacin. Alhaji Mohammed Sani Omolori, shi ne wanda ya fi zaƙewa wajen adawa da shi Attah Ibrahim.

Waɗannan dalilai su suka sabauta yin murabus ɗin Attah Ibrahim daga wannan kujera ta shugabancin Ibira a cikin shekarar 1954.

Rasuwarsa

Attah Ibrahim ya rasu a shekarar 1996.

Manazarta:


Edo V. O. (2008). The Evolution and Development of Central Administration in Ebiraland, 1920-1997. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://www.nobleworld.biz/images/Edo.pdf

Okene A.A. da Suberu O.A. (2013). The British Conquest of Ebiraland, North Central Nigeria 1886-1917: A Military Interpretation of Sources. Professor (History & International Studies) Nigerian Defence Academy Kaduna, Africa’s Top Military University PMB 2109, Kaduna – Nigeria. American International Journal of Contemporary Research Vol. 3 No. 6; June 2013.

Segun J. A. (2013). Politics and Conflicts: A Study Of Ebiraland, Nigeria (1977-2007). Department of Political Science and International Relations, School of Social Sciences, College of Development Studies, Covenant University, Ota, Nigeria.



Masarautar Okene

Sarakuna Ƙasar Ibira

Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub