Attah Omadivi Ƙasar Ibira

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Attah Omadivi 1904 - 1917 A.D.


Gabatarwa

Attah Omadivi, shi ne babban sarkin ƙasar Ibira na farko. Naɗinsa ya biyo bayan samun nasarar da Turawa suka yi a shekarar 1904.

Marubuta kamar irin su Edo (2013), Segun (2013), sun ruwaito cewa bayan samun nasarar da mayaƙan Turawa a ƙarƙashin shugabancin manjo Marsh, da laftanonin da suka haɗa da Sparrenbarg, Moran, Byng-Hall, Gallway, Smith, Oldman da kyaftin Lewis suka yi, residan na yankin Kabba, Mr. Morgan ya naɗa Omadivi a  matsayin babban sarkin ƙasar Ibira baki ɗaya da ta haɗa da garuruwan Okene, Owuda Adidi-Eika, Opoh-Obehira da kuma Apata-Ihima. Waɗannan garuruwa duk masu cin gashin kansu ne a baya kafin cin nasarar Turawan kamar yadda tsarin zamantakewar ƙasar Ibira yake.

Wannan naɗi na Omadivi sakayya ce da Turawan suka yi masa game da goyon baya da ya basu na yaƙar Agidi wanda ya jagoranci jama’ar Ibira da suka yiwa Turawan tawaye da kuma ƙoƙarin shi Mr. Morgan ɗin na mayar da mulkin ƙasar Ibira ƙarƙashin jagoranci mutum ɗaya dan su samu sauƙin mulkarsu a fakaice.

Shi Omadivi wakili ne na Ohindase Abogunde wanda shi ne babban shugaban unguwar Okengwe.

Asalin shugabancin ƙasar Ibira yana ƙarƙashin digatai shida ne da suke shugabantar unguwanni shida da suka haɗa da Okengwe, Okehi, Adavi, Eika, Ihima, da kuma Eganyi kamar yadda ya zo a Okene da Suberu (20130, Segun (2013).

Attah, shi ne taken wannan sarauta ta babban sarkin ƙasar Ibira wanda Turawa suka basu (Edo, 2013). Amma daga baya an riƙa kiran wannan sarauta da suna Ohaniyi Ebira kamar yadda yake a yanzu.

Amma duk da wannan naɗi da aka yiwa Omadivi a matsayin babban sarkin ƙasar Ibira baki ɗaya, mulkin nasa bai yi tasiri sosai a kan sauran unguwannin ba. Dalilin hakan kuwa shi ne cewa shi a lokacinsa babu hukumar nan ta mulkin gargajiya mai suna 'Native Authority' (Edo, 2013); hukumar da ta baiwa Turawa cikakkiyar damar mulkar Arewacin Najeriya a fakaice.

A yanzu duk wanda ke da wannan muƙami yana zaune ne a garin Okene wanda a yanzu shi ne yake a matsayin helikwatar mulkin ƙasar Ibira.

Omadivi ya rasu a shekarar 1917. Orudi Adano ne ya gaje wanda shima ba jimawa ya mutu.

Manazarta:


Edo V. O. (2008). The Evolution and Development of Central Administration in Ebiraland, 1920-1997. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://www.nobleworld.biz/images/Edo.pdf

Okene A.A. da Suberu O.A. (2013). The British Conquest of Ebiraland, North Central Nigeria 1886-1917: A Military Interpretation of Sources. Professor (History & International Studies) Nigerian Defence Academy Kaduna, Africa’s Top Military University PMB 2109, Kaduna – Nigeria. American International Journal of Contemporary Research Vol. 3 No. 6; June 2013.

Segun J. A. (2013). Politics and Conflicts: A Study Of Ebiraland, Nigeria (1977-2007). Department of Political Science and International Relations, School of Social Sciences, College of Development Studies, Covenant University, Ota, Nigeria.Masarautar Okene

Sarakuna Ƙasar Ibira

Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafinSauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub