Zuwan Turawa Ƙasar Ibira

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Zuwan Turawa Ƙasar Ibira


Gabatarwa

Tun kafin Turawa su shigo yankunan da a yanzu suke cikin Arewacin Najeriya, suna da masaniya game da albarkatun noma da suke samuwa a waɗannan yankuna ta hanyar kasuwancin Hamada. Wannan shi ne babban dalilin da ya saka a farkon ƙarni na goma sha tara suka kutso kai ta cikin ruwa a kan jiragen ruwa.

Wannan lamari na sha’awar ƙarfafa dangatakar kasuwanci da Birtaniya ke da shi ya faɗaɗa a tsakiyar ƙarni na goma sha tara, lokacin da kamfaninsu mai suna National African Company ya samu gindin zama a wannan yanki, kamfanin da daga baya ya rikiɗe ya koma Niger Royal Company a shekarar 1886 (Okene da Suberu, 2013).

Zamowar ƙasar Ibira guri maras nisa daga waɗannan kogunan Biniwai da Neja, da kuma Lokoja wacce take ita ce helikwatar Lardin Arewa a wannan lokacin, sannan kuma da zmowarta yanki mai dausayin noma wanda ya saka jama’ar yankin suka shahara wajen aikin noma har ta kai ga abin da suke nomawa akan fita da shi kasuwanni masu nisa musamman amfanin gona na ‘beniseed’, ya ɗauki hankalin Turawa. Saboda haka a cikin shekarar 1903, Turawa a ƙarƙashin mulkin Luguard, suka turmushe wannan yanki na Ibira ya koma ƙarƙashin mulkinsu da ƙarfin soja (Okene da Suberu, 2013).

Sai dai, tun cikin shekarar 1890, akwai dangantakar kasuwanci mai ƙarfi tsakanin manya-manyan garuruwan Ibira da suka haɗa da Okene, Eganyi da Eika Ohizeni da kuma kamfanin Turawa na Royal Niger Company wanda ke sayen manja, auduga, kernels da beniseed a hannun Ibirawa (Okene da Suberu, 2013).

Amma a ra’ayin Edo (2008), Turawan sun fara yaƙar ƙasar Ibira ne a shekarar 1902, inda yake bayyana lokacin da Turawan suka taras da Ibirawan na zaman ‘yan-marina ƙarƙashin shugabancin shugabannin dangi. Wanda daga baya Turawan suka turmushe su da ƙarfin bindiga. A bayanan nasa ya ƙara da cewa, faɗa tsakanin Turawa da Ibirawa bai ƙare ba sai a cikin shekarar 1904 wanda a lokacin ne ya ruwaito shugaban Lardin Kabba (Kabba Province) Mr. Morgan yana cewa ‘yanzu Ibira suna tsoron Turawa kuma zaman lafiya ya samu tsakanin Turawa da Ibirawa’. Biyo bayan haka kuma suka ɗanƙara musu Omadivi, shugaban ƙabilar Okengwe a matsayin babban sarkin Ibira wanda daga baya suka yiwa muƙamin nasa laƙabi da Attah.

A yunƙurinsa na haɗe ƙarfi waje guda, Morgan wanda yake shi ne shugabn Lardin Kabba, ya naɗa Attah Omadivi a matsayin Hakimin Okene, Owuda Adidi-Eika, Opoh-Obehira da kuma Apata-Ihima bisa shawarar Malcom a cikin shekarar 1904 (Segun, 2013). 

Kenan muna iya rufe wannan Rubutu da cewa Turawa sun ɗauki lokaci mai tsawo suna yunƙurin samun gidin zama a awannan ƙasa ta Ibira, amma basu fara yaƙi da su ba sai a cikin shekarar 1902 wanda kuma suka ƙarƙare a shekarar 1904.

Manazarta:


Edo V. O. (2008). The Evolution and Development of Central Administration in Ebiraland, 1920-1997. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://www.nobleworld.biz/images/Edo.pdf

Okene A.A. da Suberu O.A. (2013). The British Conquest of Ebiraland, North Central Nigeria 1886-1917: A Military Interpretation of Sources. Professor (History & International Studies) Nigerian Defence Academy Kaduna, Africa’s Top Military University PMB 2109, Kaduna – Nigeria. American International Journal of Contemporary Research Vol. 3 No. 6; June 2013.

Segun J. A. (2013). Politics and Conflicts: A Study Of Ebiraland, Nigeria (1977-2007). Department of Political Science and International Relations, School of Social Sciences, College of Development Studies, Covenant University, Ota, Nigeria.



Masarautar Okene

Sarakuna Ƙasar Ibira

Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub