Zamantakewa a Ƙasar Ibira

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Zamantakewa a Ƙasar Ibira


Gabatarwa

Zamantakewa a ƙasar Ibira ta tasirantu da yanayin ƙasar da a yau suke zaune a kanta. Kasancewar wannan yanki na ƙasar Ibira guri ne mai duwatsu, sai ya zamo suna zaune ne a kan waxannan duwatsu waxanda a kansu suka samar da gidaje har zuwa haula.

Gida a Ƙasar Ibira

Yanayin gidaje a ƙasar Ibira yakan fara ne daga gida mai ɗauke da iyalan da suka haɗa da Miji da Mata da ‘ya’ya da 'yan'uwa da kuma duk wanda sauran yardaddun maigida na daga dangi duka a cikin gida ɗaya, wanda namiji mafi yawan shekaru kan zama jagora (Segun, 2013), irin wannan gida shi suke kira Ohueje. Idan wannan gida ya bunƙasa yakan zama babban gida da suke kira Ovovu. Shi kuma Ovovu gida ne babba guda ɗaya wanda ke ɗauke da iyalin da suke da tushe ɗaya ta ɓangaren namiji (wato kakansu ɗaya ne). A cikin wannan gida akwai wasu gidajen a cikinsa (irin waɗannan gidaje a ƙasar Hausa ana kiransu waje-waje) akan samu namiji babba mafi yawan shekaru ya zama shi ne jagora wanda ke warware abubuwan da suka-je-su-zo na game da saɓani. A irin wannan babban gida akan samu har da ‘yan’uwan na ɓangaren mata suma sukan zauna a ciki (Segun, 2013). Sai dai, a ra'ayin Okene da Suberu (2013), sun ce ɓangaren waje na gidan yakan zama gurin amfanin sauran jama'a ne da ba 'yan gidan ba.

Daga waɗancan gidaje guda biyu kuma sai a samu gidan yawa (haula), gidan da suka kira Abara. Manyan gidaje (Ovuvu) biyu ko fiye da haka suke samar da wannan gida na yawa. Idan za a yanke hukunci kan wata matsala a irin wannan gidaje sai shugabannin sauran gidajen sun haɗu tukuna. Kuma mutanen da suka yarda cewa su ‘yan’uwa ne na jini suke haɗuwa waje guda. A nan ma, namiji babba wanda ya fi kowa shekaru da kuma ɗan abin hannu shi ke zama jagora. Sai dai a irin wannan mataki ba shi ke yanke hukunci na ƙarshe ba sai ya tuntuɓi sauran jagororin gidaje. Yana kuma daga cikin ɗawainiyoyinsa adana duk abin da dangin suka noma a fadarsa dan rarrabawa sauran ‘yan’uwa bisa adalci. Akan samu irin waɗannan dangi har yau, daga cikin ragowarsu akwai Etumi, Avi, Adovosi, Egiri da Ogagu (Segun, 2013; Okene da Suberu, 2013). Kowane dangi suna da inkiyar da ke zuwa a farkon sunansu. Inkiyoyin su ne Ozi, wacce ke nufin 'ya'yan da kuma Ani, wacce ke nufin jama'ar. Bayan inkiya kuma kowane dangi suna da gunki, wanda ka iya zama kodai wani abu ne kamar dutse, ko sassaƙa gunki, koma dabba wanda shi ne camfin su (Okene da Suberu, 2013).

Daga wancan mataki na dangi kuma sai a samu unguwa, irin waɗancan dangi-dangi da suke ganin cewa suna da dangatar jini ta kusa ko ta nesa (irin wanda a Hausa ake kira dangin-dangi-rere), to su suke samar da unguwa, wanda suka kira Ekura. Har yau ɗin nan akwai guda shida daga cikin irin waɗannan unguwanni (duk da cewa yanzu sun zama manyan garuruwa) waɗanda suka haɗa da: Okengwe, Okehi, Adavi, Eika, Ihima, da kuma Eganyi. Duk da cewa kowane daga cikin waɗannan unguwanni yana cin cin gashin kansa ne, amma wani abu guda kan haɗa su. Shugaban wannan unguwa shi suke kira Ohinoyi-ete, wanda za a iya bashi fassara ta digaci ko mai gari. Kowace unguwa guda ɗaya akwai dangi-dangi masu yawa a cikinta waɗanda suka yarda cewa suna da dangantaka ta jini da juna a kusa ko a nesa. Misali idan aka ɗauki Okengwe, za a samu waɗannan dangi-dangi a cikinta Akuta, Ehimozoko, Avi, Esusu, Ogu, Asuwe, Omoye, Omovi, Eira da Adobe. Shi shugaban nasu yakan tuntuɓi jagororin dangi-dangi idan wata matsala da ta shafi dangin ta taso. Kuma yana da maitaimaki da suka kira Ohireba (Okene da Suberu, 2013).

Wannan shugaba, shi ke zama babban jagora ta kowace fuska da ta haɗa da addini, siyasa da sauransu. Sun yarda cewa shi ke da dama ta yin magana da iskokansu, har ma yakan magantu da su a lokuta na musamman kamar lokacin damina dan roƙa musu albarkar ruwan sama (Okene da Suberu, 2013).

Bayan waɗannan shugabannin na dangi, kuma akan samu shugaban mayaƙa, da kuma shuwagabannin addini. Waɗannan nau’ukan shugabanni guda uku, shugaban dangi, shugaban yaƙi da shugabannin addini suke jan ragamar Ibirawa baki ɗaya. Dukkan su sukan haɗu a hubbaren gumakansu da suke kira da suna ‘Iregba’, gurin da suke bautawa gumakansu (Segun, 2013).

Tare da haɗin kan juna, waɗannan digatai guda shida suke tafiyar da ragamar shugabancin ƙasar Ibira ta hanyar tuntuɓar juna ko zama tare a lokacin da buƙatar hakan ta taso har zuwan Turawa a shekarar 1903 Miladiyya (Okene da Suberu).

Manazarta:


Abdullahi, O.E. (1992). Cultural and identity crisis among Ebira Adolescents. Ilorin Journal of Education Foundations. Journal of Faculty of Education. University of Ilorin. 12.50-55.

Abdulƙadir M.S. (2011). Islam in the Non-Muslim Areas of Northern Nigeria, c.1600-1960, Department of History, Bayero University, Kano, Nigeria. Ilorin Journal of Religious Studies, (IJOURELS) Vol.1 No.1, 2011, Pp.1-20.

Audu S.M. (2010). Politics and Conflicts in Ebiraland, Nigeria: The Need for a Centralised Leadership Since 1917.  Journal of Sustainable Development in Africa. Volume 12, No.1, 2010), ISSN: 1520-5509, Clarion University of Pennsylvania, Clarion, Pennsylvania.

Attadescendant (2013). The Ebira Traditional Marriage Rite. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: https://attadescendantforum.wordpress.com/2013/03/ 17/the-ebira-traditional-marriage-rite/

>David M.A. (2013). Ebira Youth Forum Association (E.Y.F.A). An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://ebirayouthforumassociation.blogspot.com.ng

/2013/05/history-of-ebira-people.html

Ekeh A. (2015). List of Traditional Marriage Requirements in Kogi. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: https://constative.com/people/lifestyle/list-of-traditional-marriage-requirements-in-kogi/

/>Haruna M. (2012). Historical Background of Kente (Aso-Oke) in Okene Local Government Area of Kogi State. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://culturenaija.blogspot.com.ng/2012/07/historical-background-of-kenteaso-oke.html/

Jimba M.M.M. (2012). Muslim of Kogi: A Survey. Nigeria Research Network (NRN), Oxford Department of International Deɓelopment, Queen Elizabeth House, University of Oxford/

/Kwekudee (2014). Ebira People: The Most Outspoken, Talented and Hardworking People of Kogi State In Nigeria. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://kwekudee-tripdownmemorylane.blogspot.com.ng/2014/03/ebira-people-most-outspoken-talented.html/

Lukman I. (2015) Ebira. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://docilepen.blogspot.com.ng/p/blog-page.html

Mohammed, A.R. (1984), History of the Spread of Islam in the Niger-Benue Confluence Area: Igalaland, Ebiraland and Lokoja c. 1900-1960. Ph.D thesis submitted to Bayero University, Kano.

Okene A.A. da Suberu O.A. (2013). The British Conquest of Ebiraland, North Central Nigeria 1886-1917: A Military Interpretation of Sources. Professor (History & International Studies) Nigerian Defence Academy Kaduna, Africa’s Top Military University PMB 2109, Kaduna – Nigeria. American International Journal of Contemporary Research Vol. 3 No. 6; June 2013.

Segun J. A. (2013). Politics and Conflicts: a Study of Ebiraland, Nigeria (1977-2007). Department of Political Science and International Relations, School of Social Sciences, College of Development Studies, Covenant University, Ota, Nigeria.

Segun J. A. da Samuel O. (2010). Politics, Violence and Culture: The Ebira Tao Nigeria Experience. Bassey Andah Journal Vol3.

Tenuche M.S. (2002). Intra-Ethnic Conflict and Violence in Ebira Land, from the Selected Works of Marietu S Tenuche (PhD). Kogi State University, Anyigba.

Ukonga P.F.O. (2013). The imperatives of Ebira Unity of 40 million people to the development of Ebira Nation, Nigeria and sub Saharan Africa- A realistic perspectiɓe. Lecture delivered to the Ebira summit in Okene on the 30th March 2013.

Wikipedia (2016). Ebira People. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: https://en.wikipedia.org/wiki/Ebira_peopleMasarautar Okene

Sarakuna Ƙasar Ibira

Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafinSauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub