Kasar Igala

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Ƙasar Igala


Gabatarwa

Ƙasar Igala tana cikin jahar Kogi a cikin yankin tsakiyar Arewan Najeriya. Ita ce ƙarshen yankin Gabas na jahar ta Kogi; mahaɗar kogunan Neja da Binuwai tana Yamma da ita.

Wannan ƙasa ta Igala tana da faɗin murabba’in kilomita 33,589 a kan latitude ɗin Arewa 60 10’ da kuma 60 11’ na longitude ɗin Gabas kamar yadda masanin tarihi Farfesa Ahmad Rufa’I Mohammed ya kawo a littafinsa na tarihin yaɗuwar Musulunci a garuruwan mahaɗar kogunan Neja da Binuwai wanda aka wallafa a shekarar (2014).

Wannan ƙasa shimfiɗaɗɗiyar ƙasa ce wacce ta zama ƙarshen busasshiyar ƙasar hamada ta Arewacin Najeriya sannan kuma farkon ruƙuƙin daji mai dogwayen bishiyoyi na Kudancin Najeriya. Wannan bigire nata shi bata cikakkiyar damar cin moriyar noma amfanin gona nau’uka biyu; nau’in kayan da ake nomawa a Arewacin Najeriya da kuma nau’in kayan da ake nomawa a Kudancin Najeriya. Ƙasar tana karɓar kayan amfanin gona da ake nomawa a ƙwaryar Ƙasar Hausa da suka haɗa da gyaɗa, dawa, wake, riɗi, gero da sauransu. Sannan kuma tana karɓar rogo, doya, kwakwa, roba, da sauran nau’ukan kayayyakin da ake nomawa a Kudancin Najeriya.

Wannan kyakkyawan matsugunni nata ya bata damar cuɗanya da gaurayuwa da yarurruka masu mabanbantan al’adu daban-daban. Daga Gabas da Arewa ta yi iyaka da jahohin Nassarawa da Binuwai, abin da ya bata damar gaurayuwar cuɗanya da yarrukan jahar Nassarawa da kuma Idoman jahar Binuwai. Daga Kudu kuma ta yi iyaka da garuruwan Nsuka da Anacan jahohin Inugu da Anambara, waɗanda su ne tushen Inyamurai, waɗand su kuma suna daga cikin manyan ƙabilun Najeriya guda uku. Sai kuma Yamma inda ta yi iyaka da ruwan Kogin Neja.

Idah, ita ce babbar cibiya; wato helikwatar ƙasar, garin da a nan fadar babban sarkin Igala take.

Manazarta:


Jacob A. (2014). Pre-Colonial Political Administration In The North Central Nigeria: A Study Of The Igala Political Kingdom. Department Of Political Science & International Studies, Faculty Of Social Sciences, Ahmadu Bello University, Zaria. European Scientific Journal July 2014 Edition vol. 10, No.19 ISSN: 1857 – 7881.

Mohammed A.R. (2014). History of The Spread of Islam In The Niger-Benue Confluence Area: Igalaland, Ebiraland and Lokoja c.1900-1960. Ibadan University Press PLC, Ibadan, Nigeria.

Masa-Ibi S.A. (2016). Shekarau Angyu Masa-Ibi An Autobiography of the 24th Aku Uka As Told To Danjuma A. Adamu. Able Productions and Animation Books.


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub