Jami'ar Bayero Kano

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Jami'ar Bayero Kano


Gabatarwa

Jami’ar Bayero, babbar jami’a ce mai daɗaɗɗen tarihi a Arewacin Najeriya da ma faɗin Najeriyar baki ɗaya. Ita ce jami’ar farko da aka fara kafawa a birnin Kano sannan kuma tushen dukkanin wata jami’a da ke Arewacin Najeriya. Kwalejin Ahmadu Bello (Ahmadu Bello College) da aka assasa a cikin watan Janairun shekarar 1960 a ƙarƙashin Hukumar Ilimin Yankin Arewa (Northern Regional Ministry of Education) daga baya kuma ta koma Kwalejin Abdullahi Bayero a cikin shekarar 1962, sannan ta sake komawa Kwalejin Jami’a ta Abdullahi Bayero (Abdullahi Bayero University College) har zuwa 1977 inda ta rikiɗe zuwa cikakkiyar jami’a mai cin gashin kanta; wato Jami’ar Bayero (Bayero University) da ke Kano kamar yadda take a yanzu.

Tubalin ginin tarihin duk wata jami’a da ke Arewacin Najeriya yana farawa ne daga Kwalejin Ahmadu Bello ta Kano; wadda kamar yadda aka gani a sama ta zama Jami’ar Bayero daga baya. Dalili kuma shi ne cewa wannan kwaleji aka fara kafawa a shekarar 1960 da manufa ta mayar da ita jami’a sannu a hankali wadda kuma za ta amsa

sunan Ahmadu Bello University, amma bisa wasu dalilai bayan shekaru biyu da kafuwarta sai kai tsaye aka kafa Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya wadda ta zama kamar sawun giwa ya take na raƙumi ga waccar jaririyar kwalejin da ta so bunƙasa zuwa kaiwa ga wannan gwadabe.

Rumbun Ilimi, ya ƙuduri aniyar bayar da gamsassun bayanan da ake sa ran za su ƙosar da ƙishin ruwan mai buƙatar bayanai game da wannan jami’a bakin gwargwado. Haƙiƙa, Jami’ar Bayero da ke Kano ta cancanci a kira ta uwa-mabada-mama.

Burin da muke da shi har kullum, bai wuce rubutun da mai karatu yake karantawa ya zama fitilar yaye duhu game da abin da muka yi rubutu a kansa ba; a wannan karon, Jami’ar Bayero ce da ke Kano a Najeriya. A yi karatu lafiya.

Saƙon Farfesa Sagir Adamu Abbas

Farfesa Sagir Adamu shi ne mataimakin shugaban wannan jami’a (Vice Chancellor) a halin yanzu. Ga abin da ya ce da maziyarta shafin Jami’ar tasa wadda mu kuma muka fassara shi kai tsaye zuwa Hausa kamar haka:

“Barka da zuwa Jami’ar Bayero da ke Kano, makaranta mai ɗaukar hankali, ingantaccen tarihi da kuma kyakkyawan fata a gaba, guri mafi dacewa a yi karatu domin a ginu ta fuskacin ilimi da hankali.
Jami’ar Bayero cike take maƙil da malaman da suka goge a harkar karantarwa waɗanda suke shirye wajen horas da ɗalibai zuwa matakin ƙwarewa abin da ya bambanta ta da sauran jami’o’in da ke Najeriya.
Mayar da hankalin Jami’ar Bayero zuwa kaiwa ga matakin ƙwarewa ya faro ne daga shekarar 1977 lokacin da aka mayar da ita cikakkiyar Jami’a daga tsohon matsayinta na Kwalejin Ahmadu Bello wadda aka kafa a 1960, wadda kuma shi ne maɓuɓɓugar tarihin Jami’ar ta Bayero”. Jami’ar Bayero (2021).

Daga Tushe

A cikin shekarar 1960 aka buɗe makaranta mai suna Kwalejin Ahmadu Bello (Ahmadu Bello College), wadda ita ce ta zama tubalin gina dukkan wata jami’a da a yau take faɗin Arewacin Najeriya. An kuwa gina wannan makaranta ne a daidai gurin da Makarantar Koyon Harshen Larabci (School for Arabic Studies) ta yau take a cikin ƙwaryar birnin Kano.

Hukumar Ilimin Yankin Arewa (Northern Regional Ministry of Education) da ke ƙarƙashi kulawar Ministan Ilimin Yanki, Marigayi Alhaji Isa Kaita ce ta assasa wannan makaranta da nufin sannu-a-hankali ta haɓaka zuwa jami’a. Facutly of Arts and Islamic Studies (2021), ta ruwaito tsohon Ministan Ilimin Yankin Arewa, Alhaji Isa Kaita yana cewa: “An laƙabawa wannan kwalejin sunanta ne domin yabawa nagartattun ayyukan da firimiyan Arewa, Sir Ahmadu Bello ya yi wa yankin”. Ya kuma ƙara da cewa: “Tabbas kwalejin za ta zamo jami’a ta farko a Arewacin Najeriya, idan kuma hakan ta faru, za a ambace da suna Jami’ar Ahmadu Bello (Ahmadu Bello University)”.

An kafa wannan kwaleji da manufa ta gudanar da shiri na musamman kan jarabawar G.C.E. (G.C.E. Advanced Level Programmes) a darusan da suka haɗa da: Larabci (Arabic), Nazarin Addinin Musulunci (Islamic Studies), Tarihin Musulunci (Islamic History), Hausa da kuma Adabin Turanci (English Literature). Shirin da yake daidai da shirin share fagen shiga jami’a (Remedial Studies) a yau.

Sai dai, bayan shekaru biyu da fara aiwatar da waccar kyakkyawar manufa ta kafa waccar kwaleji da nufin mayar da ita jami’a mai wancan suna sai kallo ya koma sama, inda aka kafa wata sabuwar jami’ar ta Arewacin Najeriya mai helikwata a Zariya tare kuma da yi mata suna, Jami’ar Ahmadu Bello (Ahmadu Bello University), sawun giwa ya take na raƙumi.

Wannan cigaba da aka samu, ba wai kawai ya yi wa waccar manufa waigi ba ne, a’a, ya ma canja tarihin wannan kwaleji ta farko. A sakamakon haka, sai aka sauya mata suna zuwa Kwalejin Abdullahi Bayero (Abdullahi Bayero College), wanda shi kuma sunan an bata shi ne da manufa ta girmama sunan marigayi Mai Martaba Sarkin Kano Abdullahi Bayero (1826 - 1953), wanda yake shi ne mahaifin sarakuna uku da suka biyo bayansa; Muhammadu Sanusi I (1953 - 1963), Muhammadu Inuwa Abbas (1963) da kuma (Dr.) Ado Bayero (1963 - 2014). Sannan kuma kaka ga uku; Muhammadu Sanusi II (2014 - 2019), Aminu Ado Abdullahi Bayero sarkin Kano na yanzu (2021) da kuma Alhaji Nasir Ado Abdullahi Bayero sarkin Bichi na yanzu (2021).

An sake canjawa wannan kwaleji matsugunni a cikin shekarar 1964 tare kuma da samun izinin gudanar da karatun digiri a wasu fannonin ilimi. A wannan sabon matsugunni nata da a wancan lokaci shi ne otel ɗin filin jirgin sama (Airport Hotel) wanda a yanzu sansanin sojojin sama na Kano ya maye gurbin, kwalejin ta fara ɗaukar ɗalibai goma domin gudanar da horo tare da bayar da shedar B.A. Degree. Ɗalibai sun samu nasarar kammala wannan karatu a cikin shekarar 1966 kamar yadda ya zo a shafin Intanet na Jami’ar Bayero (2021).

Lugudan wutar da baki ɗayan yankin da sabon matsugunnin makarantar yake sha a tsakiyar yaƙin basasa (1967 – 1970), ya tursasa wa makarantar canjin sheƙa zuwa matsugunninta na dindindin wanda aka fi kira da tsohon fegi; wato old site kenan a Turance.

Wannan muhalli kuwa yana nan a tsakankanin unguwannin Janbulo daga Arewa, Ƙofar Kabuga da Ƙofar Duka Wuya daga Kudu, Unguwar Kabuga daga Gabas sai kuma Unuguwar Ɗorayi da take Yamma da Jami’ar.


Fuskar Mashigar Tsohuwar Jami'ar Bayero
Hoto: Campus News

Wani cigaban ya sake zuwa ga wannan makaranta a cikin shekarar 1975 inda aka ɗaga darajarta zuwa Kwalejin Jami’a (University College) tare da izinin bayar da takardar shedar digiri a madadin Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, dalilin da ya saka aka sake sauya mata suna zuwa Kwalejin Jami’a ta Abdullahi Bayero (Abdullahi Bayero University College). Ƙari a kan haka kuma aka yi mata hukumar gudanarwa ta ƙashin-kanta.

Bayan shekaru biyu da faruwar wannan lamari; 1977, sai Allah ya sake tarfawa garin wannan makaranta nono aka mayar da ita cikakkiyar jami’a mai zaman kanta tare kuma da sake sauya mata suna zuwa Jami’ar Bayero (Bayero University), Kano, sunan da ake taƙaitawa da BUK wanda kuma har zuwa yau shi take amsawa.

Shugaban waccar tsohuwar kwalejin jami’a ta Abdullahi Bayero, Dakta Mahmud Tukur, shi Allah Ya taimaka ya kafa tarihin zama mataimakin shugaban jami’ar (Vice Chancellor) na farko.

Ɗalibai

Ya zuwa lokacin da muke yin wannan rubutu (24/09/2021), jami’ar tana da ɗaliban da yawansu ya kai dubu arba’in da tara da ɗari shida da ashiri da biyu (49,622). Tare da cewa, kaso mafi yawa na ɗaliban da yawansu ya kai dubu talatin da huɗu da ɗari takwas da casa’in da biyar masu karatun digirin farko ne a mabambantan fannoni (34,895 undergraduates), dubu tara da ɗari bakwai da goma (9,710) kuma masu karatun gaba da digiri ne (Postgraduate Studies) a mabambantan matakai. Sai kuma mutane ɗari shida da saba’in da huɗu (674) da suke a makarantar kasuwanci ta Ɗangote (Ɗangote Business School), da kuma mutane dubu huɗu da ɗari uku da arba’in da uku (4,343) da suke makarantar cigaba da karatu (School of Continuing Education), kamar yadda ya zo Jami’ar Bayero (2021).

Ma’aikata

Ta fuskacin yawan ma’aikata, wannan jami’a tana da ma’aikatan da yawansu ya kai dubu huɗu da ɗari biyar da goma sha takwas (4,518). Dubu ɗaya da ɗari biyar da saba’in da biyar (1,575) ma’aikatan fannin karantarwa ne (Academic Staff), mutum ɗari biyu (200) kuma ma’aikatan fasaha ne da suka haɗa da injiniyoyi da danginsu (Technical Staff). Sai kuma mutane dubu ɗaya da ɗari ɗaya da hamsin da biyu (1,152) da suke manyan ma’aikata ne a fannin da ba na karantarwa ba (Senior Non-Teaching Staff) da kuma ƙananan ma’aikatan da ba masu karantarwa ba (Junior Non-Teaching Staff) da yawansu ya kai dubu ɗaya da ɗari biyar da casa’in da biyu (1,592) kamar yadda ya zo Jami’ar Bayero (2021).


Fuskar Mashigar Sabuwar Jami'ar Bayero
Hoto: BUK

Rassa

Abin da ake nufi da rassa a wannan rubutu shi ne kwalejoji da tsangayun da ke cikin wannan makaranta. A wannan jami’a akwai kwalejoji da suka haɗa da:

 1. Kwalejin Kimiyyar Lafiya (College of Health Science). Ana shiga wannan kwaleji kai tsaye ta wannan adireshi: http://college.buk.edu.ng/. A ƙarƙashin wannan kwaleji akwai tsangayu guda huɗu da suka haɗa da:
  • Faculty of Clinical Sciences wadda ake shiga kai tsaye ta: http://fcs.buk.edu.ng/
  • Faculty of Dentistry wadda ake shiga kai tsaye ta http://den.buk.edu.ng/
  • Faculty of Basic Medical Sciences
  • Faculty of Allied Health Sciences
 2. Kwalejin Kimiyyar Asali da Gauraye-Gauraye (College of Natural and Pharmaceutical Sciences). Ana shiga wannan kwaleji kai tsaye ta wannan adireshi: http://buk.edu.ng/cnps/. A ƙarƙashin wannan kwaleji akwai tsangayu guda uku da suka haɗa da:
  • Tsangayar Kimiyyar Rayuwa (Faculty of Life Sciences).
  • Tsangayar Kimiyyar Famasutikal (Faculty of Pharmaceutical Sciences).
  • Tsangayar Kimiyyar Zahiri (Faculty of Physical Sciences).
 3. Tsangayar Aikin Gona (Faculty of Agriculture).
 4. Tsangayar Nazarin Addinin Musulunci da Darrusan At (Faculty of Arts and Islamic Studies).
 5. sangayar Sadarwa (Faculty of Communications).
 6. Tsangayar Kimiyyar Kwamfuta da Fasahar Sadarwa (Faculty of Computer Science and Information Technology).
 7. Tsangayar Kimiyyar Ƙasa da Muhalli (Faculty of Earth and Environmental Sciences).
 8. Tsangayar Ilmi (Faculty of Education).
 9. Tsangayar Injiniyarin (Faculty of Engineering).
 10. Tsangayar Lauyanci (Faculty of Law).
 11. Tsangayar Kimiyyar Manajiman (Faculty of Management Sciences).
 12. Tsangayar Kimiyyar Walwala (Faculty of Social Sciences), wadda ake shiga kai tsaye ta: http://sms.buk.edu.ng/

Fagagen Samun Horo

Abin da ake nufi da fagagen samun horo a wannan rubutu shi ne wani fanni da ɗalibi zai shiga wannan katafariyar jami’a ya samu horo a kai wanda a ƙarshe za a bashi takardar sheda tun daga digirin farko (Bachelor) har zuwa digirin digirgir (P.hD.).

Dongane da abin da ya shafi wannan gaɓa kuwa, wannan makaranta mai ɗimbin tarihi tana bayar da digiri na farko, ba niyu da na uku da sauran kwasakwasai a fannoni da dama. Ya zuwa lokacin kammala wannan rubutu, bamu gama tantancewa ba. Sai dai, mai karatu zai iya shiga shafin kwaleji ko tsangaya kai tsaye domin ganin irin fagagen samu horo da suke a wannan kwaleji ko tsangaya tare da fatan cewa nan ga za mu sabunta shafin.

Manazarta:

Jami’ar Bayero (2021). History, Facts & Figures. An ciro a shekarar 2021 daga shafin: http://buk.edu.ng/oldbuk/?ƙ=history

Jami’ar Bayero (2021). History Of Department _ Faculty of Arts and Islamic Studies. An ciro a shekarar 2021 daga shafin: http://www.ais.buk.edu.ng/?ƙ=node/7


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub