Gwamna Ali Sa'adu

Me ka ke nema?


Barista Ali Sa'adu Birnin Kudu


Gabatarwa

Lauya kuma ɗan siyasa, wanda aka fi sani da Barista Ali Sa’adu Birnin Kudu, wanda kuma shi ne cikakken sunansa. Shi ne gwamnan farko na farar hula a jahar Jigawa.

Haihuwa

An haife shi a garin Birnin Kudu wanda shi ne helikwatar mulkin ƙaramar hukumar Birnin Kudu  a ranar 13 ga watan Fabarairu na shekarar 1959.

Karatu

Barista Ali Sa’adu Birinin Kudu, ya yi karatunsa na firamare a garin Birnin Kudu, daga nan kuma ya samu nasarar shiga makarantar sikandire ta Birnin Kudu (Birnin Kudu Secondary School) wacce ta koma Kwalejin Gwamnati ta Birnin Kudu (Government College Birnin Kudu). Daga nan kuma ya ɗora zuwa Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya inda ya yi karatun digiri a fannin doka (Bachelor Degree in Law), sannan bayan gamawarsa da shekara guda kuma ya samu tafiya makarantar aikin doka (Law School).

Zamowarsa Gwamna

Kafin zamowarsa gwamna ya yi aiki da ma’aikatar Shari’a ta tsohuwar jahar Kano a tarayyar Najeriya na tsawon shekaru uku inda ya bari ya shiga siyasa a shekarar 1991. Ya kafa tarihin zamowarsa gwamnan farar hula na farko a Jahar Jigawa. An zaɓe shi ya zama gwamnan Jahar Jigawa a watan Disamba na shekarar 1991 a ƙarƙashin tutar jama’iyyar SDP (Social Democratic Party). Ya kama aiki a watan Janairu na shekarar 1992.

Gudunmawar da ya Bada

Ya bada gudunmawa sosai wajen gina wannan jaha ta Jigawa.

Barinsa Mulki

Mulkinsa ya ƙare a watan Disamba na shekarar 1993.


Gwamnoni


Masarautu

  • Dutse
  • Gumel
  • Hadejia
  • Kazaure
  • Ringim

Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub