Gwamna Mohammed Badaru Abubakar

Me ka ke nema?


Gwamna Mohammed Badaru Abubakar MON, MNI 2015 zuwa yau


Gabatarwa

Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, MON, MNI, hamshaƙin mai kuɗi ne, ɗan kasuwa, kuma basarake. An haife shi a shekarar 1962 a garin Ɓaɓura.

Karatu

Bayan kamala karatunsa na firamare da sikandire, ya samu nasarar shiga Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya inda ya fita da digiri a fannin Akawu (B.Sc Accounting), sannan kuma ya samu zuwa ‘National Institute for Policy and Strategic Studies (NIPSS)’.

Gogayyar Aiki

Alhaji Mohammed Badaru Abubakar wanda aka fi sani da Badaru Talamiz, gogaggen ɗan kasuwa ne, shi ne shugaban cincirindon kamafonin Talamiz Group, kamfani da ya ƙware wajen harkar sufuri, manfetur, fiton kaya, harkar muhalli, gine-gine, da sauransu.

Wannan katafaren kamfanin yana da rassa, da ‘ya’ya a ciki da wajen Najeriya, kamar irinsu Nijar, Egypt, Holland, Saudi Arabia, Belgium, da sauransu. Kamfanoni irin su ‘Talamiz Nigeria Limited, Talamiz Motors, Talamiz Consumer Company, Talamiz Transport, Talamiz Commodities, Talamiz Properties, Talamiz Poultry and Farms, Talamiz Petroleum, Talamiz Oil Mill Ltd, Socar Talamiz Ltd, da sauransu duk suna daga cikin jeren wannan cincirindon kamfanoni na Talamiz Group.

Alhaji Mohammed Badaru Abubakar mamba ne na ‘National Council on Privatization, Federal Republic of Nigeria’, sannan kuma shi ne mataimakin shugaban ‘Federation of West Africa Chamber of Commerce (FEWACCI)' wacce  take reshen ‘Chamber of Commerce in the West African region’.

Saboda gudunmawa mai gwaɓi da ya jima yana bayarwa ta fuskacin haɓɓakar tattalin arziƙi, shi yasa aka ga dacewar bashi lambar girmamawa mai taken: ‘Member of the Order of the Niger (MON)’ da kuma muƙamin ‘Sardaunan Ringim’ kuma ‘Wali of Jahun’.

Zamowarsa Gwamna

Ya samu nasarar cin zaɓen gwamna da aka gudanar a shekarar 2015 ƙarƙashin tutar jama’iyyar APC wanda haka ta mai da shi zaɓaɓɓen gwaman Jahar Jigawa mai ci yanzu.


Gwamnoni


Masarautu

  • Dutse
  • Gumel
  • Hadejia
  • Kazaure
  • Ringim

Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafinSauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub