Gwamna R. Shekoni

Me ka ke nema?


Colonel Rasheed Alade Shekoni 1996 – 1998


Gabatarwa

Kanal Rasheed Alade Shekoni, shi ne gwamnan Jahar Jigawa na Huɗu, sannan kuma na uku a gwamnan soja.

Haihuwars

An haife shi a ranar 25 ga watan Yuli na shekarar 1958 a birnin Legas.

Karatu

Kanal Rasheed Alade Shekoni ya samu nasarar halartar makarantar firamare mai suna ‘St. Peters Elementary School, Zaria’, daga nan kuma ya wuce zuwa makarantar sojoji ta Zariya inda ya yi karatunsa na sikandire. Bayan kammalawarsa daga wannan sikandire ne kuma ya samu shiga kwalejin tsaro ta Najeriya da ke Kaduna (Nigerian Defence Academy, Kaduna).

Shigarsa Aikin Soja

Ya fita daga wannan makaranta ta Sojoji da muƙamin ‘Second Lieutenant’ a shekarar 1978.  Tun daga sannan ya ci gaba da samun muƙamai daga lokaci zuwa lokaci, har sai da ya kai muƙamin kanal (colonel) a shekarar 2000. Sannan kuma ya je Jami’ar Jos inda ya fita da digiri a fannin soshiyoloji (sociology).

Ya riƙe muƙamai kamar ‘Platoon Commander’, ‘Company Commander’, ‘Administration officer Grade II’, da kuma muƙamin ‘Provost’ a helikwatar sojojin Najriya.

Zamowarsa Gwamnan Jahar Jigawa

Ya zama gwamnan Jahar Jigawa a watan Agusta na shekarar 1996.

Barinsa Aikin Soja

Da wancan babban muƙami nasa na kanal ya bar akin soja.


Gwamnoni


Masarautu

  • Dutse
  • Gumel
  • Hadejia
  • Kazaure
  • Ringim

Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafinSauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub