Gwamna Ibrahim Saminu Turaki

Me ka ke nema?


Gwamna Ibrahim Saminu Turaki, 1999 - 2007


Gabatarwa

Alhaji Ibrahim Saminu Turaki, attajiri kuma ɗan siyasa, tsohon gwamna kuma tsohon sanata. Shi ne gwamnan Jahar Jigawa na shida, sannan kuma gwamnan farar hula na biyu.

Haihuwa

An haife shi a ranar 14 ga watan Yuni na shekarar 1963 a garin Kazaure.

Karatu

A 'Kudu Central Primary School' ya yi karatunsa na firmare, daga nan kuma sai ya wuce zuwa kwalejin gwamnatin tarayya ta Kaduna (Federal Government College, Kaduna), daga nan sai makarantar share fagen shiga jami'a ta Zariya, sai kuma ya shiga Jami'ar Ahmadu Bello ta Zariya (Ahmadu Bello University, Zaria), inda ya samu Digiri.

Zamowarsa Gwamnan Jahar Jigawa

An zaɓe shi gwamnan Jahar Jigawa a ranar 29 ga watan Mayu na shekarar 1999 a ƙarƙashin tutar jama'iyyar ANPP (All Nigerian People's Party).

Gudunmawar da ya Bada

Ya bada gagarumar gudunmawa wajen haɓɓaka wannan jaha ta Jigawa a kowane fanni tare kuma da bada fifiko wajen haɓɓaka tattalin arziƙin jahar a hukumance da kuma ɗaiɗaikun jama'a. Samar da makarantar koyon kimiyyar kwamfuta mai suna 'Informatics Institute' da ke Kazaure wacce take ita ce ta farko a Najeriya da kuma cibiyar bayar da sabis ɗin Intanet ta garin Dutse mai suna 'Galaxy ITT' na daga cikin manyan nasarorin da ya samu.

Barinsa Mulki

Ya bar wannan kujera ta shugabancin Jahar Jigawa a shekarar 2007 bayan da aka gudanar da zaɓe sannan kuma ya damƙa kujerar mulkin jahar a hannun Alhaji Sule Lamiɗo, shi kuma ya wuce zuwa zauren majalisar dattawa ta tarayyar Najeriya a matsayin sanata mai wakiltar Jigawa ta Area.


Gwamnoni


Masarautu

  • Dutse
  • Gumel
  • Hadejia
  • Kazaure
  • Ringim

Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafinSauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub