Gwamna Sule Lamido

Me ka ke nema?


Gwamna Sule Lamiɗo, CON, 2007 - 2015


Gabatarwa

Shi ne gwamnan Jahar Jigawa na shida sannan kuma gwamnan farar hula na uku. Alhaji Sule Lamiɗo, gogaggen ɗan siyasa ne, wanda ya fara siyasa tun PRP ta Marigayi Malam Aminu Kano wanda a hannunsa ya koyi siyasa. Ya haura shekaru 35 yana siyasa. Shi ɗa ne ga digacin garin Bamaina. Kalmar ‘Lamiɗo’ tana nufin sarki a yaren fullanci. An haifi Alhaji Sule Lamiɗo a garin Bamaina ta cikin ƙaramar hukumar Birnin Kudu a shekarar 1948.

Karatu

Ya yi karatu a ‘Senior Primary School Birnin Kudu’ wacce yanzu ta koma ‘Government College, Birnin Kudu), daga nan kuma ya wuce zuwa Kwalejin Barewa ta Zariya (Barewa College, Zaria).

Gogayyar Aiki

Ya riƙe muƙaman siyasa da dama, tun daga PRP, SDP, har zuwa jama’iyyarsa ta yanzu wato PDP. An taɓa zaɓensa a matsayin wakili a zauren majalisar wakilai ta Najeriya (Member Federal House of Representatives) a jamhuriyya ta biyu, sannan kuma ya riƙe muƙamin Ministan Harkokin Waje na Najeriya a lokacin shugaba Olesegun Obasanjo.

Zamowarsa Gwamnan Jahar Jigawa

Ya zama gwamnan jahar Jigawa a shekarar 2007 bayan ya lashe zaɓen da aka gudanar ranar 29 ga watan Mayu na shekarar 2007 ƙarƙashin tutar jama’iyyar PDP. Haka nan kuma aka sake zaɓensa a karo na biyu a watan Afirilu na shekarar 2011 bayan cikar wa’adin mulkinsa na farko.

Gudunmawar da ya Bada

Gudunmawa da ya bayar wajen haɓɓaka Jahar Jigawa tana da wahalar ƙididdiguwa, shi ne ya gina katafariyar sakatariyar jaha (state secretariat) da ke Dutse, shi ya gina gidan radiyo da talabijin na Jigawa, shi ya samar da filin sauka da tashin jiragen sama na Jahar Jigawa, shi ya samar da Jami’ar Jahar Jigawa da ke Kafin Hausa, shi ya samar da Jami’ar Gwamnatin Tarayya ta Jigawa da ke Dutse, shi ya gina kwalejin koyon aikin jinya da ungozoma da ke Birnin Kudu, shi ya gina gidajen ƙanan hukumomi 27 da ke Dutse, shi ya gina gidajen saukar manyan baƙi (G9) na Jahar Jigawa da ke Dutse, da sauran ayyuka masu tarin yawa.

Barinsa Mulki

Ya bar wannan kujera ta gwamnan jahar Jigawa bayan cikar wa’adin mulkinsa na biyu, inda ya damƙa ragamar mulkin a hannun Alhaji Badaru Umar Ɓaɓura a shekarar 2015.


Gwamnoni


Masarautu

  • Dutse
  • Gumel
  • Hadejia
  • Kazaure
  • Ringim

Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafinSauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub