(Dr.) Shekarau Angyu, CFR

Me ka ke nema?


Shafin Farko

(Dr.) Shekarau Angyu, CFR


Gabatarwa


Dr. Shekarau Angyu Masa Ibi Kuvyo II, Aku-Uka na Wukari

Shi ne Aku-Uka na 27. Sarki ne mai daraja ta ɗaya, kuma shugaban majalisar sarakunan jahar Taraba (chairman Taraba council of chiefs).

Shine (Dr.) Shekarau Angyu Masa Ibi Kuvyo II, CFR, Aku-Uka na Wukari. Shi ne na 27 a jerin Aku-Uka da aka yi a tarihin wannan sarauta ta Aku-Uka. Sannan kuma shi ne mafi daɗewa a kan karagar mulki. Mutum ne shi mai nagarta. Yana da haƙuri, jajircewa, ƙwazon aiki, son jama’a, da kuma iya zama da jama’a. Mutum ne mai matuƙar son ci gaba a dukkan abin da ya saka a gabansa.

Yana da gogayyar rayuwar aiki tun zamanin turawa har zuwa yau ɗin nan; abin nufi shi ne cewa ya yi aiki da Turawa tun kafin samun ‘yancin kan Najeriya har zuwa bayan samun ‘yanci.

Shekarau Angyu, direban mota ne, ɗankasuwa, sannan kuma basarake. Dukkan waɗannan abubuwa da aka ambata, su ne burikan rayuwarsa, kuma Allah cikin ikonsa ya cika masa su ɗaya bayan ɗaya kamar yadda ya ambata a lokacin da yake amsa tambayar malaminsa na makaranta a lokacin da ya ke karatu a garin Lupwe ta garin Ibi, cewa, “so na ke na zama direba, ɗankasuwa sannan kuma sarki”.

Ɗan wannan rubutu da mai karatu zai karanta, taɓa-ka-lashe ne game da rayuwar wannan managarcin sarki wanda ya sauya tarihin Jukunawa da tsohuwar daular Kwararrafa a wannan zamani da mu ke ciki.

Dr. Shekarau Angyu Masa Ibi Kuvyo II, Sarki ne mai daraja ta ɗaya, kuma shugaban majalisar sarakunan jahar Taraba (chairman Taraba council of chiefs).

Haihuwa

An haifi Shekarau a ranar Lahadi 18 ga watan Afirilu na shekarar 1937; wato yau yana da shekaru 80 (1937 – 2017) cur a duniya. Shi ɗa ne ga Ashumanu II Angyu Masa Ibi; Aku-Uka na 22, wanda ya yi zamani 1940 – 1945. Sunan mahaifiyarsa Buvini Awudu. Ya fito daga zuriyar Ba-gya; ɗaya daga cikin gidajen sarautar Wukari.

Wannan suna nasa Shekarau, suna ne da ya samo asali daga Hausa. A al’adar Hausa, idan mace mai ciki ta haura wata tara bata haihu ba, to akan kira abin da ta haifa da suna shekarau idan namiji ne, mace kuma a ce da ita shekara. Wato ana nufin mutumin da ya shekara a ciki. Sunansa na yare kuma shi ne Agbunshu. Kenan, sunansa ya zama Shekarau Agbunshu.

Karatu

 1. 1950 – 1954: Makarantar Elimantare ta Wukari (Wukari Elementary School).
 2. 1954 – 1957: Babbar Makarantar Mishan ta Lapwe da ke Ibi (Missionary Senior School Lapwe).

Gogayyar Aiki

 1. 1958 – 1960: Ya yi aiki da Hukumar Gargajiya ta Wukari a matsayin Jami’in rarraba wasiƙu (mail officer), daga baya aka ɗaukaka matsayinsa zuwa jami’in sufuri; wato babban direba kenan (transport officer), sauyin da ya cika masa burinsa na farko na son zama direba.

  Ayyukansa a wannan matsayi sun haɗa da tabbatar da lafiyar dukkan ababen sufuri mallakin wannan hukuma, da kuma tabbatar da cewa an bayar da su ga wanda ya dace a duk lokacin da buƙatar amfani da su ta taso, sannan kuma a halin da za su iya amfanuwa.

 2. 1960 – 1962: Jami’in Taimako (personal assistance) ga ‘executive officer’ na ma’aikatar kula da lafiyar dabbobi (ministry of animal health) na gwamnatin arewa da ke Kaduna a wancan lokacin Dr. Samuel Ɗanjuma A. Gani.
 3. 1962 – 1963: Jami’in Taimako (personal assistance) a ofishin sakataren mulki (parliamentary secretary) na gwamnatin arewa da ke Kaduna a wancan lokacin, Ambasada Jolly Tanko Yusuf.
 4. 1963 – 1966: Jami’in Taimako (personal assistance) a ofishin shugaban ma’aikatar wutar lantarki ta Najeriya (Electricity Corporation of Nigeria), Malam Ibrahim Sangari Usman.
 5. 1966 – 1976: Jami’in Ciniki (sales manager) a gidan man-fetur na Makurɗi (Texaco filing station, Makode). Wannan sabon ci gaba da kuma sauyin aiki daga ma’aikatar gwamnati zuwa kamfani mai zaman kansa shi ne abin da ya tabbatar wa da Shekarau burinsa na biyu na son zama ɗan kasuwa.

Tun da farko, gaskiya da riƙon amana su ne halayen da suka shugabansa a ma’aikatar wutar lantarki ya ɗora shi a wannan babban matsayi a kuma wannan sabon gidan mai nasa.

Zaman shekarau a wannan kamfani ya kafa kamfanin, dan abin da ya yi ya fi ƙarfin a ce ya samar da ci gaba. Ya riƙe wannan gidan mai tun yana guda ɗaya tilo a lokacin da aka buɗe shi har ya hayayyafa tare kuma da ƙarin samar da wasu sababbin abubuwan yi da ba sayar da man-fetur ba. Daga cikin irin waɗannan ayyuka da shekarau ya shigo da su wannan kamfani akwai sabis na mota, sayar da wasu kayayyaki, yin faci da sauran su.

Sarauta

A ranar 28 ga watan Agusta na shekarar 1976, aka bayar da sanarwar naɗin Shekarau Angyu a matsayin sabon Aku-Uka na Wukari. Naɗin da ya saka shi zamowa Aku-Uka na 27 a garin na Wukari.

Wannan mataki da ya taka a rayuwa, shi ne abin da ya cika masa burinsa na ƙarshe kamar yadda ya ambata a shekaru 20 da suka gabata, cewa, yana so ya zama direba, ɗan kasuwa, daga ƙarshe kuma ya zama sarki.

Haƙiƙa wannan naɗi na Dr. Shekarau Angyu Masa Ibi Kuvyo II, ya samu karɓuwa tare kuma da amincewar ‘yan majalisar sarki kuma masu zaɓen sabon sarki guda huɗu, da kuma yarjewar iyalan gidajen sarauta guda biyu; Ba-gya (Kuvyo) da kuma Bama. Tun daga wannan lokaci zuwa yau (1976 – 2017), Dr. Shekarau Angyu shi ne Aku-Uka na Wukari. Wato kenan, zuwa yau (2017), yana da shekaru 41 a kan karagar mulkin Jukunawa mai helikwata a Wukari. Sannan kuma shi ne Aku-Uka mafi daɗewa a kan karagar mulki.


Jukunawa na gaida sarki a lokacin wucewarsa zuwa kan karaga.

Gudunmawa

Masu iya magana sun ce, mai kamar zuwa akan aika, a wani faɗi kuma suka ce kowa ma ya yi rawa bare ɗan makaɗa. Haƙiƙa wannan maganganu haka suke. Dr. Shekarau Angyu Masa Ibi Kuvyo II, mutum ne da ya samu horo tun daga tushe na yi wa jama’a hidima, sannan kuma aka yi gam-da-katar cewa mutum ne mai shawa’ar yin hakan. Wato zani ce ta taras da mu je mu.

Gudunmawa da Dr. Shekarau ya bayar a wannan gari sannan kuma cibiyar sabuwar Daular Kwararrafa, tana da tarin yawan gaske. Gari ne da ya same shi a matsayin ƙaramin gari, a yau kuma ya maishe shi katafariyar alƙariya mai kusan dukkan abubuwan da birane ke buƙata na kayan more rayuwa. Saboda haka sai dai mu ɗan tsakuro mu rubuta kamar haka:

 1. Fannin Raya Al’adu da farfaɗo da daular Kwararrafa: Haƙiƙa Dr. Shekarau Angyu Masa Ibi Kuvyo II, ya taka muhimmiyar rawa wajen sake raya al’adun Jukunawa da kuma farfaɗo da daular Kwararrafa. Tun farkon hawansa mulki yake ƙoƙari a wannan fannin har ta kai a yau ana iya tunawa da waccar tsohuwar daula ta Kwararrafa tare kuma da ganin al’adu da kyawawan halayen Jukunawa na son zaman lafiya, karɓar baƙi da sauran su. Tabbas a yau duniya tana iya banbance tsohuwar suturar Jukunawa, salon rawarsu ta gargajiya, da kuma ta zamani.
 2. Abubuwan More Rayuwa: A wannan fanni na wadata Wukari da ababen more rayuwa, kusan ana iya cewa dukkan wani abin more rayuwa da ake buƙatar sa a alƙarya, to akwai shi a wannan gari na Wukari, kamawa tun daga layukan tarho na dauri da na zamani, cibiyar aika wasiƙu, tituna, wutar lantarki, kasuwannin zamani, ababen hawa, gidajen man-fetur, manya da ƙananan otel, gidajen saukar baƙi, da sauran abubuwan more rayuwa rankacakam.
 3. Ilimi: Ilimi gishirin zaman duniya, garin Wukari, gari ne da ke cike da makarantu kamawa tun daga firamare har zuwa jami’o’i; ba fa jami’a ba, a’a, jami’o’i.  Saboda akwai jami’o’i guda biyu a garin Wukari, ɗaya ta gwamnatin tarayya, ɗayar kuma mai zaman kanta wacce ake kira Kwararrafa University. Makarantun .firamare, sikandire da kwalejoji ma kuma duk akwai su birijik a garin na Wukari.

Ɗauraya

Shekarau, ɗa ne ga Ashumanu II, Aku-Uka na 22 (1940 – 1945), mahaifiyarsa kuma sunanta Bivini Awudu. Tsohon ma’aikaci ne wanda ya fara aiki tun zamanin Turawa har zuwa bayan samun ‘yancin kan Najeriya. Shi direba ne, ɗan kasuwa, a yanzu kuma sarki.

Mutum ne nagartacce mai halaye ababen ambato. Yana son jama’a, haƙuri, juriya, jajircewa, son ciyar da jama’arsa gaba, da sauran halaye na gari wanda sanin su duka ke da kamar wuya, gurguwa da auren nesa.

Sarki ne mai daraja ta ɗaya, kuma shugaban majalisar sarakunan jahar Taraba (chairman Taraba council of chiefs).

Manazarta:


Adamu  Ɗ. A. (2016). Shekarau Angyu Masa-Ibi, An Autobiography of the 24th Aku-Uka, as Told to Ɗanjuma A. Adamu. An buga a Able Productions tare da haxin Guiwar Animation Books.

Oluyede I.O. (1996). Shaped by Destiny, A Biography of (Dr.) Shekarau Angyu Masa-Ibi, Kuvyo II, The Aku Uka of Wukari. University of Ilorin.

Tattaunawa da (Dr.) Shekarau Angyu, Masa-Ibi, Kuvyo II, Aku Uka na Wukari, a ranar Asabar 19/08/2017, a fadarsa da ke Wukari

Masarautar Wukari

Sarakunan jukunawa


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafinSauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub