Majalisar Sarkin Jukunawa

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Majalisar Sarkin Jukunawa


Gabatarwa

Majalisar sarki; wato majalisar Aku-Uka, majalisa ce da ta ƙunshe da mutane guda biyar; shi Aku-Uka (Sarki) kansa, Abon Acio (Waziri), Abon Ziken (Galadima), Kinda Acio (Sarkin Gida) da kuma Kinda Ziken (Sarkin bai).

  1. Aku-Uka: Shi ne kankat a masarautar Jukun. Matsayinsa ne sama da kowane muƙam. Shi ne mai shiga tsakanin allolin Jukunawa da kuma sauran al’ummar Jukunawa. Shi kaɗai yake iya magana da allolin Jukunawa sannan ya sanar da mabiya abin da ya dace.
  2. Abon Acio (Waziri): Shi yake da ikon gudanar da duk wani aiki da Aku-Uka zai yi matuƙar Aku-Uka ɗin baya nan ko kuma yana halin rashin lafiyar da za ta hana shi gudanar da fada.
    Sannan shi ke bai wa sarki shawara a harkokin al’adu da kuma al’amuran yau-da-kullum. Yana da damar gudanar da shari’ar da ta shafi auratayya kai tsaye ba tare da ya tuntuɓi sarki ba. Amma kuma duk da haka, waziri baya gadon kujerar Aku-Uka.
  3. Abon Ziken (Galadima): Galadima shi ne mataimakin  waziri, sannan kuma mai gadon kujerarsa da zarar babu kowa a kanta. Yana taimaka wa waziri wajen gudanar da ayyukan da suka shafi sarauta.
  4. Kinda Acio (Sarkin gida): Shi ne mai kula da al’amuran cikin gidan Aku-Uka. Yana kuma aiwatar da wasu ayyukan na fannin sarauta, sannan kuma yana da mataimaka masu  riƙe da ƙananan muƙaman sarauta.
  5. Kinda Ziken (Sarkin bai): Shi ne shugaban masu riƙe da ƙananan muƙaman sarauta.

Manazarta


Adamu D.A. (2016). Shekarau Angyu Masa-Ibi An Autobiography of the 24th Aku-Uka As Told to Ɗanjuma A. Adamu. Able Productions in Collaboration with Animation Books.

NNPC (2007). Hausa da Maƙwabtansu. Northern Nigerian Publishing Company, Zaria, Kaduna State, Nigeria.

Sanusi N.M. (2009). Stories of Dutse Palace 1421 – 2009. Jigawa State Printing Press, Dutse, Jigawa State, Nigeria.


Masarautar Wukari

Sarakunan jukunawa


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafinSauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub