Yaququwan Jukanawa

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Zaɓen Sarkin Jukanawa


Gabatarwa

Jukunawa, mutane ne jarumai, kuma masana salo-salon yaƙi. Sune suka shugabancin daular gamayyar mayaƙan Kwararrafa. Sun yi yaƙuƙuwan da ba za a iya ƙididdige yawansu ba. Sun yaƙi Ƙasar Hausa tun daga Dutse har zuwa Gobir. Kuma sun yi galaba a kan manya-manyan masarautun Ƙasar Hausa da suka haɗa da Kano, Katsina da kuma Zazzau.

Jukunawa ko Kwararrafa, sun yi yaƙi na tsawon shekaru 72 da wasu daga cikin garuruwan Hausa. An fara yaƙin tun zamanin Aku-Uka Angyu Katakpa daga shekarar 1599 har zuwa waɗanda suka biyo bayansa a shekarar 1671, zamanin Aku-Uka Daju. Sannan kuma sun yaƙi daular Barno a shekarar 1680 sun kuma yi galaba a kanta. Akwai wannan magana a cikin littafin tarihin rayuwar Aku-Uka na yanzu, (Dr.) Shekarau Angyu Masa-Ibi, Kuvyon II, wanda aka wallafa a shekarar 2016.

Wannan labari na yaƙuƙuwan Jukunawa da manyan masarautun Ƙasar Hausa ya zo a wasu littattafan tarihi da dama. Daga ciki akwai Mai Martaba Sarkin Dutse, Nuhu Muhammadu Sanusi da ya labarta rasuwar sarkin Dutse na 13, Mantau Jarmai Babba cewa: “Ya mutu a yaƙin Kwararrafa tare da wasu mutane masu yawa waɗanda suka tafi yaƙin tare da shi”.

Hakanan kuma, NNPC (2007), sun labarta cewa, Kwararrafa ta yaƙi Kano a zamanin sarkin Kano na 27, Muhammadu Zaki ɗan Kiske (1582 – 1618). Sun kuma sake yaƙar garin na Kano a karo na biyu zamanin sarkin Kano na 34, Muhammadu Kukuna (1652 – 1660). Sannan kuma su sake komowa a karo na huɗu zamanin sarkin Kano na 36, Daɗi Ɗan Bawa (1670 – 1703). A dukkan waɗannan yaƙuƙuwa guda uku da aka ambata, ruwayar ta nuna an galabci Kano ne matuƙar galaba ta inda har ta kai ga sarakunan na Kano sun gudu sun bar garin.

A ɗaya daga cikin irin waɗannan yaƙuƙuwa ne su Kwararrafawa suka ja wa sarkin Kano kunne cikin harshensu na Jukunanci da cewa “Iri ya Kasen”, wanda daga baya aka jirkita shi ya zama sunan wata unguwa a garin na Kano mai suna Yakasai. Ma’anar waccar kalma ta Jukunawa ita ce “Za mu dawo”.

Haka nan kuma akwai wata unguwa a cikin birnin Zazzau mai suna Tudun Jukun, wacce ake dangata ta da share guri zaunan da su Jukunawan suka yi bayan sun ci birnin na Zazzau da yaƙi.

Babbar manufar Kwararrafa ta yin waɗacan yaƙuƙuwa ita ce tabbatar da adalci ba faɗaɗa daula ba. Ga abin da Aku-Uka ya faɗi a cikin littafin tarihinsa: “Ya kamata a san cewa, Jukunawa basu yaƙi biranen Ƙasar Hausa da manufar gudanar da mulkin-mallaka na har abada ba, sai don su nuna musu cewa akwai maza bisa kansu” Adamu (2016). Sannan kuma ya ci gaba da cewa: “Iya tsawon tarihin yaƙuƙuwan da kakanninmu suka yi da Ƙasar Hausa, basu taɓa kwasar ganima daga can Ƙasar Hausa sun zo da ita matsugunninsu da yake ƙasan Kogin Binuwai ba”.

A bisa waɗannan hujjoji na ke son taƙaita rubutun nawa da cewa, lallai tarihi ya nuna an yi waɗannan yaƙuƙuwa, kuma daga cikin abubuwan da suka faru, za mu iya fahimtar gaskiyar maganar zamowar Jukunawa mutane jarumai masu dabarar yaƙi.

Manazarta


Adamu D.A. (2016). Shekarau Angyu Masa-Ibi An Autobiography of the 24th Aku-Uka As Told to Ɗanjuma A. Adamu. Able Productions in Collaboration with Animation Books.

NNPC (2007). Hausa da Maƙwabtansu. Northern Nigerian Publishing Company, Zaria, Kaduna State, Nigeria.

Sanusi N.M. (2009). Stories of Dutse Palace 1421 – 2009. Jigawa State Printing Press, Dutse, Jigawa State, Nigeria.


Masarautar Wukari

Sarakunan jukunawa


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafinSauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub