Zaɓen Sarkin Jukanawa

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Zaɓen Sarkin Jukanawa


Gabatarwa

A al’adance, idan aka samu gurbi a fadar Jukunawa, sakamakon mutuwa ko wani dalili na daban, dattawa masu zaɓen sarki za su bayar da umarni ga gidajen sarautar Jukunawa guda biyu; wato zuriyar Bagya da ta Bama, cewa su fitar da sunayen waɗanda suke ganin su suka cancanta su nemi wannan kujera ta sarautar Jukunawa. Idan suka samu waɗannan sunaye, sai kuma su bi matakan da aka saba da su wajen zaɓe da kuma naɗin sabon sarki kamar haka:

Daren litinin

Matakin farko daga cikin jerin matakan da dattawan Jukunawa ke bi wajen zaɓen sabon sarki shi ne kwana a garin Adi Bakundi a daren Litinin da su masu neman kujerar suke yi. A wannan mataki ana umartar dukkan masu sha’awar neman wannan kujera ta Aku-Uka su fita daga garin Wukari zuwa garin Adi Bakundi a daren litin, su kwana a can.

Zaɓe

Bayan an kwana ɗaya a Adi Bakundi, sai kuma a ayyana wata rana guda ɗaya da za a yi zaɓen sarkin a cikinta. Idan ranar ta zo, sai su waɗannan ‘yan takara da suka kwana a Adi Bakundi su rankaya zuwa wani guri da ake kira Avi.

A wannan guri dukkan ‘yan takarar za su yi shigar fararen kaya (Zani da hula). Wannan shiga ana kiranta da Nbufyo a harshen Jukunanci. Bayan sun yi wannan shiga sai kuma a zaɓi ɗaya daga cikinsu bisa la’akari da waɗannan siffofin da za a zayyana:

Babban abin da dattawa masu zaɓen sarkin Jukun suke lura da shi, shi ne halaye na gari waɗanda dama tun samartakar ‘ya’yan sarki ake lura da waɗannan halaye tare da su. Daga ciki akwai:

  1. Kawo arziƙi da wadata a dukkan faɗin ƙasar Jukun: Dattawan suna lura da cewa, dukkan ɗan sarki da za a zaɓa zai kawo ƙaruwar arziƙi da wadata ta hanyar samun damina mai yawan ruwan da zai samar da kaka mai albarka, zaman lafiya, haɗin kai da kuma kwanciyar hankali.
  2. Sannan ɗan sarkin ya zamo mai gujewa aikata laifuffuka.
  3. Ya zamo mai girmama na gaba da shi.
  4. Ya zamo mai tattali da kuma kiyaye shigar al’ada ta sarauta.
  5. Ya zamo mai kyawawan halayen da za su zama abin koyi a rayuwarsa ta sarauta da kuma ɗaiɗaiku.

Idan suka laluba suka tabbatar da waɗannan halaye a tare da ɗaya daga cikinsu, wanda dama kamar yadda na ambata tun samartakarsu ake lura da su, to sai a ayyana shi a matsayin zaɓaɓɓen Aku-Uka. Daga nan kuma sai abubuwa su ci gaba kamar haka:

Ziyarar Ɗakin Bauta

Bayan an zaɓi sabon Aku-Uka, sai kuma ya yi shigar baƙaƙen kaya shi kaɗai. Zai ɗaura baƙin zani sannan ya saka baƙar hula. Sai kuma ya shiga ɗaki mai tsarki da ake kira Kunvyi a Jukunanci.

Zaɓen Suna

Bayan zaman sabon Aku-Uka a ɗaki mai tsarki, sai kuma ya hau farin doki daga garin Avyi ya tafi Kuntsa. A wannan gari na Kuntsa ne zai zauna a kan fatar damisa, a kawo masa sunayen da sai Aku-Uka ne kaɗai yake amsa su, ya zaɓi guda ɗaya daga ciki. Sunayen su ne: Agbumanu, Awudumanu, Ahumanu, da kuma Kuvyon.

Kuntsa, suna ne na babban shugaba mai tsarki, wanda yake bai wa Aku-Uka waɗancan sunaye ya zaɓi ɗaya daga ciki, sannan kuma bayan ya zaɓa ya damƙa masa kayayyakin sirrin sarauta (Kamar a ce tagwayen masu da ake bayarwa a Kano), waɗanda mai riƙe da su shi ne sarki.

Zaɓen Mata

A bisa al’adar Jukunawa, zaɓaɓɓen sabon sarki yana gadar ɗaya daga cikin matan tsohon sarkin da ya gada idan har mutuwa ya yi. Wannan al’ada kuma ana gudanar da ita a garin Puje. Wannan mata ita ake kira Wakuku.

Saboda haka bayan an kammala dukkanin ayyukan al’ada da ya kamata a yi a Kuntsa, sai kuma sarki da tawagarsa su zarce zuwa Puje, a nan za a fito masa da matan tsohon sarkin ya zaɓi guda ɗaya daga ciki wacce za ta zamar masa uwar-gida.

Hikimarsu ta yin wannan al’ada ita ce cewa, ita wannan mata ta tsohon sarki ta riga ta zauna a gidan sarauta tare da tsohon sarki, saboda haka ta koyi zama da sarki, su kuma matan sabon sarkin da za su shigo basu da wannan gogayya, saboda haka ita sai ta koyar da su yadda ake kula da sarki, da kuma zaman gidan sarauta.

Shiga Fada

Mataki na ƙarshe a jerin abubuwan da ake yi a zaɓen sarkin Jukunawa shi ne shigar sarki fada. Bayan sarki ya zaɓi mata daga cikin matan tsohon sarki, sai matar ta kintsa kayanta ta baro Puje zuwa Wukari, idan ta zo ita za ta tarbi sarki tare da sauran masu riƙe da sarautun gargajiya na Jukunawa a wani bigire da ake kira Afyin Acio.

Daga nan kuma sai sabon Aku-Uka ya zarce zuwa wani wajen bauta domin gudanar da ziyarar ban girma ga allansu mai suna Yaku. Shi Yaku, shi ne allan da yake bai wa Jukunawa kariya a lokutan yunwa da kuma annoba.

Bayan an kammala wannan ziyarar ban girma, sai kuma sabon Aku-Uka ya shiga fadarsa ta mulki da take a babban birnin Jukunawa wato Wukari.

Wannan shi ne abin da aka saba da shi a tsarin naɗin sarautar Jukanawa a bisa turbar kaka-da-kakanni.

Bayan Zuwan Turawa

Da Bature ya zo ya kafa mulkinsa na mallaka a wannan ƙasa ta Najeriya, sai yanayi da tsarin yadda ake gudanar da zaɓe da naɗin sarakuna ya sauya. Wannan sauyi ya shafi Jukunawa.

Kundin tsarin mulkin Najeriya yanzu ya bai wa gwamnan jaha damar amincewa da kuma watsi da sunan sarkin da masu zaɓen sabon sarki suka miƙa masa. Saboda haka sai aka samu ƙarin matakai guda biyu a bisa yadda aka saba, da farko akwai miƙa sunan sarkin ga gwamnatin jaha domin tantancewa da zarar an zaɓa, sai kuma naɗi bayan an kammala gudanar da waɗancan al’adu da aka ambata a sama.

Idan masu zaɓen sabon Uka-Uka suka zaɓe shi, to za su tura sunan zuwa ga gwamnan jahar Taraba kenan a yau. Idan gwamnan ya karɓi wannan suna, shike nan sai a ci gaba da gudanar da waɗancan al’adu da na ambata a sama.

Sai kuma, mataƙi na ƙarshe da ya taɓa wancan tsohon tsari wanda shi ne na naɗi. Bayan an kammala dukkan waɗancan shagulgula, sai kuma gwamna ya zo ya rantsar da sarki a fadarsa.

Waɗannan su ne abubuwa biyu da suka shigo cikin sabgar zaɓe da naɗin sabon sarki wato Aku-Uka a ƙasar Jukunawa.

Manazarta


Adamu D.A. (2016). Shekarau Angyu Masa-Ibi An Autobiography of the 24th Aku-Uka As Told to Ɗanjuma A. Adamu. Able Productions in Collaboration with Animation Books.

NNPC (2007). Hausa da Maƙwabtansu. Northern Nigerian Publishing Company, Zaria, Kaduna State, Nigeria.

Sanusi N.M. (2009). Stories of Dutse Palace 1421 – 2009. Jigawa State Printing Press, Dutse, Jigawa State, Nigeria.


Masarautar Wukari

Sarakunan jukunawa


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub