Zaman Majalisa Sarkin Jukun

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Zaman Majalisa Sarkin Jukun


Gabatarwa

Dukkan wasu shari’o’i, dokoki da kuma zartar da su a wannan babbar masarauta mai daɗaɗɗen tarihi, ana yin su ne bisa tuntuɓar juna a lokuta daban-daban na zaman fada. Mafiya muhimmanci daga cikin waɗannan lokuta na zaman fada su ne lokutan safiya, hanti da kuma maraice.

Zaman Safe

A safiyar kowace rana, Aku-Uka yana zama a wata fadarsa da ke cikin gidansa, talakawa su zo su gaishe shi sannan  kuma a labarta masa abubuwan da suka gudana a ciki da wajen fadarsa. Waɗanda suke ƙarƙashin ikonsa da waɗanda suka fi ƙarfin ikonsa kamar irinsu rasuwa, haihuwa, aure, abubuwan da ke gudana a jaha da ma ƙasa baki-ɗaya.

Daga cikin irin waɗannan abubuwa akwai waɗanda suke buƙatar saka hannunsa akwai kuma waɗanda basu shafe shi ba. Kowane Bajukune yana da damar halartar wannan zama na fada. Ana kiran wannan zama Kyoma a Harshen Jukunawa.

Zaman Hantsi

Wannan zama shi ne Gyo. Zama ne da masu riƙe da muƙaman sarautar gargajiyar Jukunwa ke hallaruwa a gaban Aku-Uka domin karɓar ayyukan da za su gudanar a wannan rana.

Zaman Maraice

Agyedi, shi ne sunan da ake kiran wannan zama. ‘yan majalisar sarki da dattawan Jukunawa masu zaɓen sarki ke aiwatar da wannan zama. Ana gudanar da wannan zama a  ɗakin sirri a cikin fadar Aku-Uka. A wannan zama ne ‘yan majalisar sarki tare da haɗin guiwar dattawan Jukunawa ke tattaunawa tare kuma da ɗaukar mataki a kan duk wani abu da ya shafi masarautar.

Bayan masu gudanar da wannan zama sun gama tattaunawa, sun kuma tsayar da shawara game da wani al’amari, sai kuma waziri ya shiga wajen sarki ya sanar da shi sakamakon wannan tattaunawar, dukkan hukuncin da sarki  ya yanke, shi waziri shi zai sake komawa ga ‘yan majalisa ya sanar da su.

Manazarta


Adamu D.A. (2016). Shekarau Angyu Masa-Ibi An Autobiography of the 24th Aku-Uka As Told to Ɗanjuma A. Adamu. Able Productions in Collaboration with Animation Books.

NNPC (2007). Hausa da Maƙwabtansu. Northern Nigerian Publishing Company, Zaria, Kaduna State, Nigeria.

Sanusi N.M. (2009). Stories of Dutse Palace 1421 – 2009. Jigawa State Printing Press, Dutse, Jigawa State, Nigeria.


Masarautar Wukari

Sarakunan jukunawa


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafinSauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub