Manjo Abba Kyari

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Manjo Abba Kyari


Gabatarwa

An haifi Manjo Abba Kyari a ranar 17 ga watan Nuwamba na shekarar 1938, a garin Dikwa da ke kan iyakar Najeriya da Nijar.

Ya zama gwamnan jahar Kaduna 1967 – 1975.

Karatu

Ya fara karatu a ‘Damasak Elementary School’, daga nan kuma ya wuce zuwa ‘Borno Middle School’, sai kuma ‘Government College. Zaria’. Bayan kammala wannan kuma sai ya wuce zuwa ‘Royal Officer’s Training School’ da ke Teshie ta ƙasar Ghana, sannan sai ‘MON Officer Cade School’ da ke ƙasar Birtaniya a shekarar 1959 zuwa 1960. Sannan kuma ya je ‘School of Infantry’ da ke Westiminister ta ƙasar Amurka, sannan kuma ya je ‘Missiles School’ da ke Fortisili ta Jahara Oklahoma ta ƙasar Amurka.

Zamowarsa Gwamna

Ya riƙe muƙamai da dama a gidan soja kafin zamowarsa gwamnan Jahar Tsakiyar Arewa (North Central State) a shekarar 1967.

Manazarta:


Kaduna State Ministry of Budget and Planning. (2016). Kaduna State in Perspective 6th Edition. Multimate Inv. Nig. Limited, Kinkino Road, Kaduna-Nigeria.

Kaduna State Ministry of Economic Planning. (2013). Kaduna State Government, State Development Plan, 2014-2018.

Haruna M. (Ba Rana). People and Politics, a (Brief) History of Kaduna: the city of crocodiles. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://www.gamji.com/haruna/haruna251.htm

Wikipedia (2016). Kaduna State. An ciro a shekarar (2016), daga shafin: www.wikipedia.com

Bello da Oyedele (1970).Cities of the Savannah (Babu gurin bugu).Gwamnonin Kaduna

Masarautu


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:

       

Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub