Ibrahim Muhmud Alfa

Me ka ke nema?


Shafin Farko


Ibrahim Mahmud Alfa


Gabatarwa

An haife shi a ranar 14 ga watan Agusta na shekarar 1942 a garin Garkiɗa ta tsohuwar jahar Gwangola wacce kuma yanzu take cikin jahar Adamawa.

Karatu

Ibrahim Alfa, ya fara karatunsa daga makarantar firmare ta "Jimeta Central Primary School" da ke Jimetan Yola a shekarar 1948, daga nan kuma sai "Yola Middle School" a shekarar 1960, daga nan kuma sai kwalejin Barewa ta Zariya a shekarar 1962.

Aikin Soja

Ibrahim Mahmud Alfa ya shiga aikin sojan saman Najeriya a watan Agusta na shekarar 1963, inda ya samu horon farko a makarantar horas da sojojin sama ta Kaduna daga watan Agusta na 1963 zuwa watan Fabarairu na shekarar 1964. Daga nan kuma sai horo a kan "Jet Aircraft" a ƙasar Jamani (Germany) a shekarar 1964 zuwa 1965, sannan kuma ya samu horo a kan tuƙa jirgin sama sojoji a Tarayyar Jahohin Amurka (USA) a shekarar 1965 zuwa 1968.

Bayan waɗannan karatuttuka kuma dai ya halarci wasu kwasa-kwasai masu tarin yawa daga ciki akwai "MIG 15" da "MIG 18" a Tarayyar Rasha (USSR), sannan kuma ya yi kwas ɗin "T.28 Instructor" da kuma "T.28 Advanced Gunnery Course" a ƙasar Amurka daga 1972 zuwa 1973.

Muƙamai

Ibrahim Alfa. ya riƙe muƙamin ofisan tashin jirage (Flying Office) a shekarar da ya dawo daga Rasha, sannan kuma ya a zama kwamandan reshe na rundunar sojan saman Najeriya (NAF Detachment) da ke Binin (Benin) a lokacin yaƙin basasa. Sannan kuma ya zama mamba a babbar majalisar sojan Najeriya a shekarar 1975. Sannan kuma ya riƙe muƙamin "Air Officer Operation" a shekarar 1981.

Zamowarsa Gwamna

Guruf Kyaftin Ibrahim Mahmud Alfa psc, ya zama gwamnan jahar Kaduna a shekarar 1978 har zuwa 1979. Bayan barinsa kujerar gwamna, ya zama shugaban rundunar sojan sama na Najeriya (Chief of Air Staff) a ranar 1 ga watan Janairu na shekarar 1984, a lokacin shugabancin Janaral Muhammadu Buhari.

Ya bar aikin gwamnati yana da muƙamin "Air Marshal" mai riƙe da muƙamin babban shugaban sojojin saman Najeriya (Chief of Air Staff) a shekarar 1990.

Rasuwarsa

Ya rasu a ranar 16 ga watan Maris na shekarar 2001, bayan ‘yar gajeruwar rashin lafiya.

Manazarta:


Kaduna State Ministry of Budget and Planning. (2016). Kaduna State in Perspective 6th Edition. Multimate Inv. Nig. Limited, Kinkino Road, Kaduna-Nigeria.

Kaduna State Ministry of Economic Planning. (2013). Kaduna State Government, State Development Plan, 2014-2018.

Haruna M. (Ba Rana). People and Politics, a (Brief) History of Kaduna: the city of crocodiles. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://www.gamji.com/haruna/haruna251.htm

Wikipedia (2016). Kaduna State. An ciro a shekarar (2016), daga shafin: www.wikipedia.com

Bello da Oyedele (1970).Cities of the Savannah (Babu gurin bugu).Gwamnonin Kaduna

Masarautu


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:

       

Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub