Kanal Hamid Ali

Me ka ke nema?


Shafin Farko


Hameed Ibrahim Ali


Gabatarwa

Kanal Hameed Ibrahim Ali mutumin Bauchi ne. An haife shi a ranar 15 ga watan Janairu na shekarar 1955. Kanal Hameedu Ibrahim Ali, tsohon soja ne kuma ɗan siyasa mai goyon bayan Janar Muhammadu Buhari. Ya zama gwamnan jahar Kaduna a watan Agusta na shekarar 1996, sannan kuma ya bari a watan Agusta na shekarar 1998.

Bayan barinsa aikin soja, ya zama sakataren Ƙungiyar Dattawan Arewa (Arewa Consultative Forum). Yanzu haka kuma shi ne shugaban rundunar kwastam ta Najeriya (Comptroller General of the Nigerian Customs Services). Shugaba Muhammadu Buhari ya yi masa wannan muƙami a ranar 25 ga watan Agustan 2015.

Manazarta:


Kaduna State Ministry of Budget and Planning. (2016). Kaduna State in Perspective 6th Edition. Multimate Inv. Nig. Limited, Kinkino Road, Kaduna-Nigeria.

Kaduna State Ministry of Economic Planning. (2013). Kaduna State Government, State Development Plan, 2014-2018.

Haruna M. (Ba Rana). People and Politics, a (Brief) History of Kaduna: the city of crocodiles. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://www.gamji.com/haruna/haruna251.htm

Wikipedia (2016). Kaduna State. An ciro a shekarar (2016), daga shafin: www.wikipedia.com

Bello da Oyedele (1970).Cities of the Savannah (Babu gurin bugu).Gwamnonin Kaduna

Masarautu


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:

       

Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub