Manjo Hassan Usman Katsina

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Manjo Hassan Usman Katsina 1966 – 1967


Gabatarwa

Manjo Hassan Usman Katsina, shi ne gwamnan farko ɗan ƙasa na Lardin Arewa (Northern Region). An haife shi a garin Katsina a shekarar 1933. Ya fito daga gidan sarautar Katsina. Shi ɗa ne ga sarkin Katsina Usman Nagogo, shi kuma Usman Nagogo ɗan sarkin Katsina Muhammadu Dikko ne.

Karatu

Ya yi karatu a makarantar ‘Elementary’ ta Kankiya, daga nan kuma ya je ‘Katsina Middle School’ sai kuma ‘Barewa College, Zaria’, daga nan kuma sai ‘Nigerian Institute of Arts, Sciences and Technology Zaria’.

Shigarsa Soja

Ya shiga aikin soja a shekarar 1956. Bayan shigar tasa aikin soja ya sake samun damar halartar wasu kwasa-kwasai da dama a ciki da wajen Najeriya.

Zamowarsa Gwamna

Manjo Hassan Usman Katsina ya zama gwamnan soja na farko na Lardin Arewa (Northern Region) a shekarar 1966 ranar 17 ga watan Janairu. Ya bar aikin gwamnati a shekarar 1975.

Bayan wannan kuma ya bada gudunmawa wajen kafa jama’iyyar siyasa ta NPN da kuma haɗa kwamatin ‘yan ƙasa masu kishi (Committee of Concern Citizens).

Rasuwarsa

Ya rasu a ranar 24 ga watan Yuni na shekarar 1995.

Manazarta:


Kaduna State Ministry of Budget and Planning. (2016). Kaduna State in Perspective 6th Edition. Multimate Inv. Nig. Limited, Kinkino Road, Kaduna-Nigeria.

Kaduna State Ministry of Economic Planning. (2013). Kaduna State Government, State Development Plan, 2014-2018.

Haruna M. (Ba Rana). People and Politics, a (Brief) History of Kaduna: the city of crocodiles. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://www.gamji.com/haruna/haruna251.htm

Wikipedia (2016). Kaduna State. An ciro a shekarar (2016), daga shafin: www.wikipedia.com

Bello da Oyedele (1970).Cities of the Savannah (Babu gurin bugu).



Gwamnonin Kaduna

Masarautu


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:

       

Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub