Kanal Lwal Ja'afaru Isa

Me ka ke nema?


Shafin Farko


Kanal Lawal Jafaru Isa


Gabatarwa

Kanal Lwal Ja’afaru Isa mutumin Kano ne. An haife shi a ranar 20 ga watan Maris na shekarar 1950.

Karatu

Lawal Ja;afaru Isa, ya yi karatunsa na firamare a makarantar firamare ta Shahuci, daga shekarar 1961 zuwa 1965. Daga nan kuma ya samu nasarar shiga makarantar sikandiren gwamnati da ke Birnin Kudu (Birnin Kudu Secondary School), ya yi karatu a wannan makaranta daga shekarar 1965 zuwa 1969. Daga nan kuma sai Makarantar Tsaron Najeriya (Nigerian Defence Academy) da ke Kaduna, a shekarar 1970. Ya fita a ranar 30 ga watan Yuni na shekarar 1975 da matsayin 'Second Lieutenant'.

Bayan waɗannan karatuttuka da ya yi, ya kuma samu nasarar halartar wasu kwasa-kwasai a ciki da wajen Najeriya. Kaɗan daga ciki shi ne cewa ya halarci 'Junior Staff College' ta soja a shekarar 1979, sannan kuma ya je 'Senior Staff College' a shekarar 1985.

Bayan samu horon soja, ya samu nasarar zuwa jami'ar Albuquerque da ke New Mexico da kuma Jami'ar Jahar Kent duk a ƙasar Amurka daga shekarar 1980 zuwa 1984 inda ya samu digirin farko 'Bachelor of Science in Clinical Psychology and Criminal Justice Administration'. Sannan kuma ya samu digiri na biyu 'Masters of Arts in International Relations and Higher Educational Administration'.

Gogayyar Aiki

Ya riƙe ƙanana da manyan muƙamai kafin zamowarsa gwamnan Kaduna. Daga ciki akwai '1st Combatant Registrar NDA Kaduna' daga Yuni 1989 zuwa Satumba 1990. Sannan ya zama mataimakin shugaban sojan ƙasan Najeriya (Military Assistant to Chief of Army Staff) tun daga Satumba na 1990 har zuwa 1996, muƙamin da daga kansa aka yi masa gwamna.

Zamowarsa Gwamnan Kaduna

Kanal Lawal Ja'afaru Isa ya zama gwamnan soja na jahar Kaduna a shekarar 1996 ƙarƙashin shugabancin Ibrahim Badamasi Babangida.

Barinsa Aikin Soja

Ya bar aikin soja yana da muƙamin 'Brigadier General' a gidan soja cikin shekarar 2003.

Manazarta:


Kaduna State Ministry of Budget and Planning. (2016). Kaduna State in Perspective 6th Edition. Multimate Inv. Nig. Limited, Kinkino Road, Kaduna-Nigeria.

Kaduna State Ministry of Economic Planning. (2013). Kaduna State Government, State Development Plan, 2014-2018.

Haruna M. (Ba Rana). People and Politics, a (Brief) History of Kaduna: the city of crocodiles. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://www.gamji.com/haruna/haruna251.htm

Wikipedia (2016). Kaduna State. An ciro a shekarar (2016), daga shafin: www.wikipedia.com

Bello da Oyedele (1970).Cities of the Savannah (Babu gurin bugu).Gwamnonin Kaduna

Masarautu


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:

       

Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub