Sir Kashinm Ibrahim

Me ka ke nema?


Shafin Farko


Sir Kashim Ibrahim


Gabatarwa

Malamin Makaranta, kuma ɗan siyasa, sannan kuma basarake mai muƙamin Shettima, kuma marubuci. An haifi Sir Shettima Kashim Ibrahim a ranar 10 ga watan Yuni na shekarar 1910, a garin Gargar ta yankin Yerwa ta Jahar Borno. Shi ne ɗan ƙasa na farko da ya zama gwamnan yankin arewa (Northern Nigeria) wanda ke da helikwata a Kaduna.

Karatu

Ya yi karatunsa na Ƙur’ani da fannin Arabiyya tun yana ƙaraminsa. Daga baya kuma bayan ya girma aka saka shi a makarantar ‘Borno Provincial Scbhool’ a shekarar 1922. Daga nan kuma sai ya wuce ‘Katsina Training College’ inda ya kammala a 1929.

Gogayyar Aiki

Ya fara aikin karantarwa a shekarar 1929, wato kenan a shekarar da ya kammala karatunsa na kwaleji, tun daga sannan yake wannan fanni na karantarwa har sai da ya kai matsayin ‘Senior Visiting Teacher and Education Officer’ na lardin Barno.

Ya shiga harkokin siyasa a shekarar 1951. Ya samu nasarar cin zaɓen wakili a zauren majalisar yankin Arewa (Northern Nigeria) da ke da helikwata a Kaduna. Sannan kuma an naɗa shi a matsayin ministan tarayyar Najeriya na ‘Social Services’ daga baya kuma aka canja shi zuwa ministan ilimi.

Zamowarsa Gwamna

A shekarar 1962 ya zama gwamnan yankin arewa (Northern Nigeria) har zuwa watan Janairu na shekarar 1966.

Bayan siyasa kuma shi marubuci ne. Ya rubuta littattafai da suka haɗa da ‘Teacher Guide’, Littattafan lissafi cikin harshen Kanuri daga na ɗaya zuwa na huɗu, da kuma ‘Kanuri Reader for Elementary Schools’.

Rasuwarsa

Sir, Shettima Kashim Ibrahim ya rasu a ranar Laraba 25 ga watan Yuni na shekarar 1992.

Manazarta:


Kaduna State Ministry of Budget and Planning. (2016). Kaduna State in Perspective 6th Edition. Multimate Inv. Nig. Limited, Kinkino Road, Kaduna-Nigeria.

Kaduna State Ministry of Economic Planning. (2013). Kaduna State Government, State Development Plan, 2014-2018.

Haruna M. (Ba Rana). People and Politics, a (Brief) History of Kaduna: the city of crocodiles. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://www.gamji.com/haruna/haruna251.htm

Wikipedia (2016). Kaduna State. An ciro a shekarar (2016), daga shafin: www.wikipedia.com

Bello da Oyedele (1970).Cities of the Savannah (Babu gurin bugu).Gwamnonin Kaduna

Masarautu


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:

       

Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub