Dabo Muhammad Lere

Me ka ke nema?


Shafin Farko


Dabo Mohammed Lere


Gabatarwa

Alhaji Mohammed Dabo Lere haifaffen garin Lere ne da ke ƙaramar hukumar Lere ta Jahar Kaduna. An haife shi a ranar 15 ga watan Maris na shekarar 1940.

Karatu

‘Lere Junior Primary School’, daga nan kuma sai ‘Middle School, Zaria’, daga nan kuma sai ‘Provincial School, Zaria’, daga nan kuma Government College, Zaria’, daga nan kuma sai Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya. Ya fita da digiri a fannin ‘Business Administration’ da muƙamin ‘B.Sc (Hons)’.

Gogayyar Aiki

Ya yi aiki da kamfani ‘Lever Brothers’ a matsayin ‘District Sales Manager’, sai kuma ‘Cement Company of Northern Nigeria’ da irin muƙaminsa na baya, sai kuma ‘Associated Traction Limited’, sai kuma ‘Nigerian National Supply Company Limited,. Daga ƙarshe kuma ya kafa nasa kamfanonin, daga cikinsu akwai ‘Lereco Nigeria Limited’.

Zamowarsa Gwamnan Kaduna

Alhaji Mohammed Dabo Lere, ya zama zaɓaɓɓen gwamnan Jahar Kaduna a watan Satumba na shekarar 1991. An zaɓe shi a ƙarƙashin tutar jama’iyyar ‘National Republican Convention (NRC)’. Ya riƙe wannan kujera ta gwamna har zuwa watan Nuwamba na shekarar 1993.

Manazarta:


Kaduna State Ministry of Budget and Planning. (2016). Kaduna State in Perspective 6th Edition. Multimate Inv. Nig. Limited, Kinkino Road, Kaduna-Nigeria.

Kaduna State Ministry of Economic Planning. (2013). Kaduna State Government, State Development Plan, 2014-2018.

Haruna M. (Ba Rana). People and Politics, a (Brief) History of Kaduna: the city of crocodiles. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://www.gamji.com/haruna/haruna251.htm

Wikipedia (2016). Kaduna State. An ciro a shekarar (2016), daga shafin: www.wikipedia.com

Bello da Oyedele (1970).Cities of the Savannah (Babu gurin bugu).Gwamnonin Kaduna

Masarautu


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:

       

Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub