Ahmed Muhammaed Makarfi

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Alhaji Ahmed Muhammad Maƙarfi


Gabatarwa

An haifi Alhaji Ahmed Muhammad Maƙarfi a garin Maƙarfi ta Jahar Kaduna a ranar 8 ga watan Agusta na shekarar 1956.

Karatu

Ya yi makarantar firamare a makarantar firamare ta L.E.A. da ke Maƙarfi a shekarar 1965. Sannan kuma ya shiga Sikandiren Gwamnatin Tarayya (Federal Government College) da ke Inugu, ya kuma gama a 1973. Daga nan kuma sai ‘School of Basic Studies,Ahmadu Bello University Zaria’, a shekarar 1978, sannan kuma sai ‘Institute of Administration A.B.U., Zaria’ daga 1979 zuwa 1982.

Yana da takardun shedar karatu da suka haɗa da ‘First School Leaving Certificate’, ‘West African School Leaving Certifficate, Division One’, UMB, ‘Bachelor of Science in Accounting’, da kuma ‘Master of Science in Accounting and Finance’.

Gogayyar Aiki

Ya yi ayyuka da dama, ya fara da aiki da‘Nigerian Universal Bank Ltd’wanda ya riƙe muƙamin mataimakin babban manaja, sannan kuma sai karantarwa a jami’ar da ya gama daga 1985 zuwa 1987, ya kuma zama kwamashinan ‘Finance and Economic Planning’ a shekarar 1994, a lokacin gwamna Lawal Ja’afaru Isa, da sauran muƙaman da ya riƙe masu tarin yawa.

Zamowarsa Gwamnan Kaduna

An zaɓi Alhaji Ahmed Muhammad Maƙarfi a matsayin gwamnan jahar Kaduna a ranar 9 ga watan Janairu na shekarar 1999, an kuma rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu na 1999. Sannan kuma an sake zaɓarsa a matsayin gwamnan jahar Kaduna karo na biyu a shekarar 2003. Ya samu kafa tarihin cewa ya zuwa lokacin rubuta wannan tarihi nasa (2016), shi kaɗai ne gwamnan farar hula da ya samu yin zangon mulki na biyu a jere, a jahar Kaduna tun daga farkon kafata har zuwa yau.

Sanata

Bayan barinsa kujerar gwamna kuma, an zaɓe shi wakili a majalisar dattawan Najeriya, majalisar da ake kira majalisar sanatoci, tun daga 2003 har zuwa 2011. Guguwar sauyi ta shugaba Buhari, ita ta sauke shi ƙasa.

Manazarta:


Kaduna State Ministry of Budget and Planning. (2016). Kaduna State in Perspective 6th Edition. Multimate Inv. Nig. Limited, Kinkino Road, Kaduna-Nigeria.

Kaduna State Ministry of Economic Planning. (2013). Kaduna State Government, State Development Plan, 2014-2018.

Haruna M. (Ba Rana). People and Politics, a (Brief) History of Kaduna: the city of crocodiles. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://www.gamji.com/haruna/haruna251.htm

Wikipedia (2016). Kaduna State. An ciro a shekarar (2016), daga shafin: www.wikipedia.com

Bello da Oyedele (1970).Cities of the Savannah (Babu gurin bugu).Gwamnonin Kaduna

Masarautu


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:

       

Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub