Arc Mohammed Namadi Sambo

Me ka ke nema?


Shafin Farko


Arc Mohammed Namadi Sambo


Gabatarwa

Ƙwararren mai zana taswirar gidaje, tsohon gwamnan Jahar Kaduna, sannan kuma tsohon mataimakin shugaba Ƙasar Najeriya. An siffanta shi da cewa mutum ne mai haƙuri da kuma ƙwazo.

An haife shi a birnin Zariya ta jahar Kaduna a ranar 2 ga watan Agusta na shekarar 1952.

Karatu

Ya yi karatunsa na firamare a makarantun ‘Baptist Primary School, Kaduna’, ‘Kobi Primary School, Bauchi’, da kuma ‘Towns School No. 1, Zaria’, duk daga shekarar 1967 zuwa 1971. Sannan kuma ya yi sikandiren gwamnati ta Zariya (Government Scondary School Zaria), wacce yanzu ta koma kwalejin Alhuda-huda, Zariya. Daga nan kuma ya shiga ‘School of Basic Studies, Ahmadu Bello University Zaria’, daga nan kuma sai ‘Department of Architecture, Ahmadu Bello University, Zaria’ inda ya fita da digiri a fannin zana taswirar gidaje (Bachelor of Science Degree with honours in Architecture), sannan kuma ya yi karatun digiri na biyu a dai wannan fanni na zana taswirar gidaje a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, ya samu kwalin ‘Masters Degree in Architecture’ a shekarar 1978.

Gogayyar Aiki

Ya fara aiki a matsayin mai zana taswirar gida da sabuwar jahar Bauchi, inda ya yi aiki tare da wannan jaha tun daga 1976 har zuwa 1981. Ya kuma yi aiki da ‘Fulani Construction Company’ a Gombe, a matsayin manajan darakta na wannan kamfanin, daga nan ya bari ya koma ‘Ella Wiziri Associates’ a matsayin babban mai zana musu taswirar gidaje (Senior Architecct). Bayan barinsa wannan kamfanin kuma sai ya kafa nasa mai suna ‘COPLAN Associates’. An kuma yi masa kwamishinan Gona (Commissioner for Agriculture) na jahar Kaduna a watan Faburairu na shekarar 1986 har zuwa 1988, inda daga nan aka canja shi zuwa ‘Ministry of Works, Transport and Housing’.

Ya bar wannan aiki na gwamnati a shekarar 1990, ya sake komawa kan aikinsa na kamfaninsa, a lokaci guda kuma yana harkokin siyasa.

Zamowarsa Gwamnan Kaduna

An zaɓe shi gwamnan a Kaduna a watan Mayu na shekarar 2007 ƙarƙashin tutar jama’iyyar PDP. Ya bar wannan kujera kafin ƙarewar wa’adin mulkinsa

Mataimakin Shugaban Ƙasa

Alhaji Namadi Sambo ya samu ɗaukakuwa daga kujerarsa ta gwamna kafin ƙarewar wa'adin mulkinsa zuwa matakin mataimakin shugaban ƙasa bayan rasuwar shugaban Najeriya Umaru Musa ‘Yar’aduwa. Ya riƙe wannan kujera ta mataimakin shugaban Najeriya tun daga 2010 har zuwa 2015, lokacin da babbar jama’iyyar adawa ta wannan lokacin, wato APC, ta samu nasarar lashe zaɓen da aka gudanar a wannan shekara da rinjaye a dukkan kujeru, kamawa tun daga kansila har zuwa shugaban ƙasa.

Manazarta:


Kaduna State Ministry of Budget and Planning. (2016). Kaduna State in Perspective 6th Edition. Multimate Inv. Nig. Limited, Kinkino Road, Kaduna-Nigeria.

Kaduna State Ministry of Economic Planning. (2013). Kaduna State Government, State Development Plan, 2014-2018.

Haruna M. (Ba Rana). People and Politics, a (Brief) History of Kaduna: the city of crocodiles. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://www.gamji.com/haruna/haruna251.htm

Wikipedia (2016). Kaduna State. An ciro a shekarar (2016), daga shafin: www.wikipedia.com

Bello da Oyedele (1970).Cities of the Savannah (Babu gurin bugu).



Gwamnonin Kaduna

Masarautu


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:

       

Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub