Malam Nasir El-Rufa'i

Me ka ke nema?


Shafin Farko


Malam Nasir Ahmed El-Rufa'i, OFR


Gabatarwa

An yi masa sheda da jajircewa kan al’amura. Shi marubuci ne, kuma ɗan siyasa, mutum ne da tsoro ya yi ƙaranci a wajensa idan ba a ce bai san shi ba samsam. Malam Nasir El-Rufa'i mutum ne mai fasaha, da kuma hazaƙa.

An haife shi a garin Daudawa ta cikin ƙaramar hukumar Faskari da ke Jahar Katsina. An haife shi a ranar 16 ga watan Fabarairu na shekarar 1960. Mahaifinsa ya rasu lokacin yana ɗan shekaru takwas da haihuwa. Saboda haka ya girma a hannun kawunsa da ke Kaduna.

Karatu

Bayan gama karatunsa na firamare, ya samu nasarar shiga kwalejin Barewa da ke Zariya. A wannan mataki na sikandire, waccar fasaha tasa da muka bayyana a sama ta fara bayyana, inda ya fita da sakamako mai daraja ta ɗaya a jarabawarsa ta ‘WAEC’, wato ya samu ‘Distinction’ ko ‘A’ a shekarar 1976. Haka nan ma kuma a digirinsa na farko da ya yi Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya a fannin Safiyo ‘Quantity Surveyor’, ya fita da digiri mai daraja ta farko wato ‘First Class Honour’, inda ya samu takardar sheda mai taken ‘B.Sc Quantity Surveying’.

Bayan wani ɗan lokaci yana aikace-aikace tare da gwamnati wani lokacin kuma da kamfanoni masu zaman kansu, ya samu nasarar fita waje karatu, inda ya je ‘Harvard Business School’ da kuma Jami’ar Georgetown’ duka a ƙasar Amurka, inda ya yi karatun ‘Postgraduate Program’. Ya kuma samu digirin ‘LLB Degree’ daga Jami’ar Landan a watan Agusta na shekarar 2008 inda ya fita da digiri mai daraja ta ɗaya a rukuni na biyu (Second Class Upper Division) ya kuma ɗora wajen neman digiri na biyu (Masters Degree in Public Administration) shi kuma a ‘John F. Kennedy School of Government' da ke jami’ar Harvard ta ƙasar Amurka a shekarar 2009. Sannan kuma ya karɓi takardar sheda ta ‘Kennedy School Certificate in Public Policy and Management’.

Gogayyar Aiki

Alhaji Nasir Muhammad El-Rufa’i, ya yi ayyuka da dama kamawa tun daga kamfanoni masu zaman kansu har zuwa ma’aikatun gwamnati. Yana daga cikin mutane huɗu da suka kafa kamfanin safiyo da kula da kwangilar gine-gine a shekarar 1982. Wannan kamfani nasu ya shahara wajen kula da ayyukan gine-gine na gidaje da kuma tituna a duk faɗin Najeriya. Sannan kuma ya riƙe muƙamin ‘DG of Bureau of Public Enterprises, BPE’ da kuma  sakataren hukumar sayar da kadarorin gwamnatin tarayyar Najeriya (Secretary to the National Council of Privatization) daga 1999 zuwa 2003. Ya kuma riƙe muƙamin Ministan Babban Birnin Tarayyar Najeriya, Abuja.

Shi ne mutumin da har gobe Abuja take kukan rabuwa da shi, sannan kuma a lokaci guda take kwaɗayin komawarsa. Shi ya ɗaukaka darajar Abuja ta amsa sunanta na birni. A lokacin da yake riƙe da ministan Abuja, sannan kuma shi yake kula da ma’aikatar kasuwanci (Ministry of Commerce), ya yi haka har sau biyu. Sannan kuma ya kula da ma’aikatar cikin gida (Ministry of Interior). A lokacin da yake wannan aiki ya jagoranci samar da tsarin ‘Mortgate System’, bayar da katin shedar zama ɗanƙasa (Nationa ID Card), da kuma tsarin haɓɓaka samar da wutar lantarki(Electric Supply Improvement Project), da kuma sayar da gidajen gwamnatin tarayya (Sales of Federal Government Real Estates) da ke Abuja.

Zamowarsa Gwamnan Jahar Kaduna

Zaɓen da aka gudanar a shekarar 2015, shi ya bashi nasarar zamowa gwamnan Jahar Kaduna a ƙarƙashin tutar jama’iyyar APC.

Tun hawansa wannan kujera yake yunƙurin ganin Jahar Kaduna ta ci gaba, saboda haka ake yi masa kirari da mai rusau, katafila sarkin aiki, da sauransu. Saboda jajircewarsa wajen ganin kowa ya bi doka-da-oda a faɗin jahar Kaduna.

Manazarta:


Kaduna State Ministry of Budget and Planning. (2016). Kaduna State in Perspective 6th Edition. Multimate Inv. Nig. Limited, Kinkino Road, Kaduna-Nigeria.

Kaduna State Ministry of Economic Planning. (2013). Kaduna State Government, State Development Plan, 2014-2018.

Haruna M. (Ba Rana). People and Politics, a (Brief) History of Kaduna: the city of crocodiles. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://www.gamji.com/haruna/haruna251.htm

Wikipedia (2016). Kaduna State. An ciro a shekarar (2016), daga shafin: www.wikipedia.com

Bello da Oyedele (1970).Cities of the Savannah (Babu gurin bugu).


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub