Kanal Abubakar Tanko Ayuba

Me ka ke nema?


Shafin Farko


Kanal Abubakar Tanko Ayuba


Gabatarwa

Kanal Tanko Ayuba mutumin Zuru ne ta cikin jahar Kebbi. An haife shi a ranar 12 ga watan Afirilu na shekarar 1945 a garin Zuru.

Karatu

Ya halarci ‘Nigerian Military School, Zaria’ da kuma ‘Nigerian Defence Academy, Kaduna’ a 1967, daga nan kuma sai Ingila a 1970 inda ya halarci makarantar ‘School of Signal’, sai kuma ‘Army South-Eastern Signal School,  Fort Gorbob, Georgia, USA’ a shekarar 1972 zuwa 1973, sannan kuma ya je ‘Command and Staff College, Jaji, Kaduna-Nigeria’, sai kuma ‘Nigerian School of Infantry Military, Jaji, Kaduna-Nigeria’, sai kuma ‘Military College of Communication Engineering, India’ a 1981, sannan kuma ya je ‘Administrative and Staff College of Nigeria (ASCON), Badagire, Legos-Nigeria’ a 1981, sai kuma ‘Nigerian Army Intelligence School, Apapa, Lagos-Nigeria’ a 1983, sannan kuma ya je ‘National Institute for Policy and Strategic Studies (NIPSS), Kuru-Jos, Plateu-Nigeria’ a 1988.

Gogayyar Aiki

Ya shiga aikin soja a shekarar 1967, a rundunar sojan Najeriya, ya kuma riƙe muƙamai da dama tun daga ƙanana har zuwa kan zamowarsa ministan Sadarwa na Najeriya daga shekarar 1985 zuwa 1987, ‘Director of Planning Nigerian Army Headquaters, Lagos’.

Zamowarsa Gwamnan Kaduna

Ya zama gwamnan jahar Kaduna a watan Agusta na shekarar 1990, a ƙarƙashin shugabancin shugaba Ibrahim Badamasi Babangida, muƙamin da ya riƙe har zuwa shekarar 1992 inda ya damƙa mulki a hannun zaɓaɓɓen gwamnan farar hula Alhaji Mohammed Dabo Lere.

Manazarta:


Kaduna State Ministry of Budget and Planning. (2016). Kaduna State in Perspective 6th Edition. Multimate Inv. Nig. Limited, Kinkino Road, Kaduna-Nigeria.

Kaduna State Ministry of Economic Planning. (2013). Kaduna State Government, State Development Plan, 2014-2018.

Haruna M. (Ba Rana). People and Politics, a (Brief) History of Kaduna: the city of crocodiles. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://www.gamji.com/haruna/haruna251.htm

Wikipedia (2016). Kaduna State. An ciro a shekarar (2016), daga shafin: www.wikipedia.com

Bello da Oyedele (1970).Cities of the Savannah (Babu gurin bugu).



Gwamnonin Kaduna

Masarautu


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:

       

Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub