Kanal Umar Faruq Ahmed

Me ka ke nema?


Shafin Farko


Kanal Umaru Faruƙ Ahmed


Gabatarwa

Mutumin Katsina ne. An haife shi a ranar 12 ga watan Agusta na shekarar 1953.

Karatu

Ya yi karatunsa na firmare a makarantar firamare ta Giɗaɗo da ke Katsina, inda ya kammala a shekarar 1960. Daga nan kuma sai kwalejin gwamnati da ke Kaduna (Government College Kaduna), ya kammala wannan makaranta a shekarar 1966. Daga nan kuma sai ya shiga makarantar Fasaha ta Kaduna (Kaduna Polytechnic) wacce aka fi kira da (Kadpoly), ita kuma a shekarar 1972 ya gama. Daga nan kuma sai ya shiga makarantar Tsaro ta Najeriya (Nigerian Defence Academy) Wacce aka fi kira da (NDA), da ke Kaduna. Ya kammala a shekarar 1973.

Gogayyar Aiki

Kanal Umaru faruƙ Ahmed, ya riƙe manyan muƙamai a gidan soja, ya zama ‘Platoon Commander’ daga 1976 zuwa 1977, sai kuma ‘Adjuntant’ 1977 zuwa 1979, sai kuma kwamanda na Bataliya daga 1979 zuwa 1981, sai kuma ‘GSO 3 Training/Operations’ daga 1981 zuwa 1983, sai kuma ya zama ‘Military Assistant Army Headquaters’ daga 1984 zuwa 1985, har zuwa muƙaminsa na ƙarshe kafin zamowarsa gwamna wanda shi ne ‘CO 333 Maiduguri’ daga 1995 zuwa 1996.

Zamowarsa Gwamna

Kanal Umar Faruƙ Ahmed ya fara zama gwamnan 'Cross River' daga 1996 zuwa 1998 kafin a turo shi zuwa kujerar gwamnan Kaduna a shekarar 1998.

Barinsa Aikin Soja

Kanal Umar Faruƙ Ahmed ya bar aikin soja da wannan muƙami nasa na Kanal (Colonel) a shekarar 1999, bayan da ya damƙa mulki a hannun zaɓaɓɓen gwamnan farar hula, Alhaji Dr. Ahmed Muhammad Maƙarfi.

Manazarta:


Kaduna State Ministry of Budget and Planning. (2016). Kaduna State in Perspective 6th Edition. Multimate Inv. Nig. Limited, Kinkino Road, Kaduna-Nigeria.

Kaduna State Ministry of Economic Planning. (2013). Kaduna State Government, State Development Plan, 2014-2018.

Haruna M. (Ba Rana). People and Politics, a (Brief) History of Kaduna: the city of crocodiles. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://www.gamji.com/haruna/haruna251.htm

Wikipedia (2016). Kaduna State. An ciro a shekarar (2016), daga shafin: www.wikipedia.com

Bello da Oyedele (1970).Cities of the Savannah (Babu gurin bugu).Gwamnonin Kaduna

Masarautu


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:

       

Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub