Win Usman Jibril

Me ka ke nema?


Shafin Farko


Win. Usman Jibril


Gabatarwa

An haife shi a ranar 30 ga watan Yuni na shekarar 1942.

Karatu

Ya halarci ‘Nassarawa Elementary School’ da ke Abuja. Daga nan kuma sai ‘Kaduna Government College’.

Shigarsa Aikin Soja

Da ya fito daga kwaleji sai kuma ya shiga ‘Royal Canadian Flying Instruction School’, daga nan kuma ya wuce zuwa ‘Royal Canadian School of Technique’, sai kuma ya shige zuwa ‘Staff College’ da ke Bracknell ta ƙasar Ingila, daga shekarar 1970 zuwa 1971, sannan kuma sai ‘Supersonic Fighter Instruction School’ da ke Tarayyar Sobiyat (USSR), sannan kuma ya je ‘Royal Air force Staff College’ da ke Tarayyar Turai (UK), sannan kuma ya je ‘Nigerian Air force Training College, Kaduna’ a 1965.

Gogayyar Aiki

Ya riƙe muƙamai da dama kafin zamowarsa gwamnan Tsakiyar Arewa mai helikwata a Kaduna a shekarar 1975. Yana riƙe da wannan muƙami aka canjawa jahar suna ta koma jahar Kaduna (Kaduna State) kamar yadda take a yau. Saboda haka ya kafa tarihin cewa shi ne gwamnan Jahar Tsakiyar Arewa na ƙarshe, sannan kuma gwamnan Jahar Kaduna na farko.

Ya bar aikin gwamnati yana da muƙamin Group Captain a soja.

Manazarta:


Kaduna State Ministry of Budget and Planning. (2016). Kaduna State in Perspective 6th Edition. Multimate Inv. Nig. Limited, Kinkino Road, Kaduna-Nigeria.

Kaduna State Ministry of Economic Planning. (2013). Kaduna State Government, State Development Plan, 2014-2018.

Haruna M. (Ba Rana). People and Politics, a (Brief) History of Kaduna: the city of crocodiles. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://www.gamji.com/haruna/haruna251.htm

Wikipedia (2016). Kaduna State. An ciro a shekarar (2016), daga shafin: www.wikipedia.com

Bello da Oyedele (1970).Cities of the Savannah (Babu gurin bugu).Gwamnonin Kaduna

Masarautu


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:

       

Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub