Dr. Mukhtar Ramalan Yero

Me ka ke nema?


Shafin Farko


Dr. Mukhtar Ramalan Yero


Gabatarwa

An yi masa sheda da cewa, shi mutum ne mai haƙuri da kuma kawaici, da kuma biyayya ga na gaba da shi. Sannan kuma mai saka alheri da alheri. Alhaji (Dr.) Mukhtar Ramalan Yero, Akawu ne, kuma ɗan siyasa, sannan kuma basarake, yana da muƙami na 'Dallatun Zazzau'.

Haihuwarsa

An haife Alhaji (Dr.) Mukhtar Ramalan Yero a Birnin Zariya a ranar 1 ga watan Mayu na shekarar 1968 a Unguwar Ƙaura da ke cikin Birnin Zaria.

Karatu

Ya yi firamare a makarantar firamare ta L.E.A. da ke Ƙaura daga 1974 zuwa 1980. Ya kuma shiga Sikandiren Gwamnati da ke Ikara daga 1980 zuwa 1985, sannan kuma sai Sikandiren Gwamnati ta Zariya daga 1985 zuwa 1986. Ya kuma yi 'Diploma' a fannin Banki a Jami'ar Ahmadu Bello ta Zariya, sannan kuma ya samu digiri a fannin akawu (B.Sc Accounting) a shekarar 1991 daga Jami'ar Ahmadu Bello ta Zariya, sai kuma Digiri na biyu (Masters in Business Administration) duk a Jami'ar Ahmadu Bello ta Zariya. Sannan kuma ya samu shedar aikin Akawu mai taken 'Certified Public Accountant'.

Gogayyar Aiki

Ya fara aiki da Jami'ar Ahmadu Bello ta Zariya a matsayin 'Higher Executive Officer Bursary Department' a shekarar 1993, daga nan kuma ya wuce zuwa 'Universal Bank Limited' a matsayin sufabesa na akawu (Accountant Supervisor). A shekarar 1997 ya samu aiki da kamfani mai zaman kansa wato 'Nalado Nigerian Limited' a matsayin babban akawu (Chief Accountant) inda daga baya kuma aka ɗaga matsayinsa zuwa daraktan kuɗi da mulki (Director Finance and Administration) a shekarar 2007.

Mataimakin Gwamna

An ɗaukaka darajarsa zuwa mataimakin gwamnan Kaduna a shekarar 2010 bayan da Mr. Patrick Ibrahim Yakowa ya zama gwamna.

Zamowarsa Gwamnan Kaduna

Haka nan kuma rasuwar Mr. Patrick Ibrahim Yakowa ta mai da shi gwamnan Kaduna, a shekarar 2012. Muƙamin da ya riƙe har zuwa 2015.

Manazarta:


Kaduna State Ministry of Budget and Planning. (2016). Kaduna State in Perspective 6th Edition. Multimate Inv. Nig. Limited, Kinkino Road, Kaduna-Nigeria.

Kaduna State Ministry of Economic Planning. (2013). Kaduna State Government, State Development Plan, 2014-2018.

Haruna M. (Ba Rana). People and Politics, a (Brief) History of Kaduna: the city of crocodiles. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://www.gamji.com/haruna/haruna251.htm

Wikipedia (2016). Kaduna State. An ciro a shekarar (2016), daga shafin: www.wikipedia.com

Bello da Oyedele (1970).Cities of the Savannah (Babu gurin bugu).Gwamnonin Kaduna

Masarautu


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:

       

Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub