Me ka ke nema?


Shafin Farko

Hawan Daushe


Gabatarwa

Hawan Daushe, hawa ne da aka fara yin sa a zamamin sarkin Kano Usmanu I. Kamar yadda sunan yake, an yi hawan ne saboda wani shamakin sarki mai suna Haruna Daushe.

Yadda abin ya samo asali shi ne cewa, akwai wani shamakin Sarkin Kano Usman I, mai suna Haruna Daushe da ya kamu da rashin lafiyar da ta hana shi zuwa masallacin idi a ranar salla. Saboda wannan dalili sai ya zama ba a yi hawan idi da shi ba. Washegari da ya samu lafiya sai ya je zaman fada kamar yadda aka saba. Da ya je gaishe da sarki, sai yake gaya wa sarki cewa shi jiya bai samu zuwa masallaci ba ballatana ya samu hawa saboda rashin lafiya. Ya gama faɗin haka sai sarki ya tambaye shi cewa: “Yanzu ka samu lafiyar da za ka iya hawa?” Sai ya bayar da amsa da cewa ya samu. Sai sarki ya ƙara cewa da shi: “To yau za a yi maka naka hawan”.

Shike nan bayan an tashi daga zaman fada an yi sallar Azahar, sai sarki ya sa aka yi ta harba bindiga hakimai suka fito aka hau.

Da aka hau, sai sarki ya fita ta Ƙofar Ƙwaru, ya ja ya tsaya aka yi Jafi. Daga nan sai ya kaɗa linzami zuwa Yamma, sannan ya karya Kudu ya shiga Gwangwazo; wacce a wancan lokacin ake kira Tafasa, unguwar da mahaifiyar sarki; wato mai babban ɗaki take da zama. Sunanta na asali kuma shi ne A’ishatu Shekura kamar yadda ya zo a Gwangwazo (2004), yana isa ƙofar gidan sai ya tsaya, sannan ya sauka ya shiga ya gaishe ita.

Bayan sarki ya fito sai ya sake hawa ya kuma nufi Ƙofar Kudu. Da isar sa sai ya ja ya tsaya ba tare da ya sauka ba. A nan kuma sai sauran mahaya suka riƙa zuwa suna yi wa sarki jinjina. Da aka ƙare duka, sai sarki ya ja ya shiga gida sauran jama’a ma kowa ya tafi nasa gidan.

Manazarta:


Gwangwazo (2004). Gamzaki mai Asubahi, In Ya fito Gari Ya Waye, Sarkin Kano Alhaji (Dr.) Ado Bayero.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub