Me ka ke nema?


Shafin Farko

Hawan Nassarawa


Gabatarwa

Hawa ne da sarki yake yi daga gidansa zuwa gidan sarki da ke Nassarawa sannan zuwa gidan gwamna.

Shi ne hawa na huɗu a hawan sallar Azumi. Ana yin sa a rana ta huɗu ga salla. Ranar farko Hawan Idi, rana ta biyu Hawan Daushe, rana ta uku ranar hutu, a rana ta huɗu kuma sai sarki ya yi wannan hawa.

Sarki yana fita daga gida ta Ƙofar Kudu. Daga nan sai ya saka gabansa Gabas ya hau kan Titin Jaha (State Road), ya fita ta Ƙofar Nassara, ya runtuma ya je Gidan Nassarawa sannan ya tsaya. Sai ya sauka, sauran mahaya kuma su dakwance shi. Idan ya shiga na wasu ‘yan mintuna sai kuma ya fito ya sake hawa ya wuce zuwa gidan gwamnati.

A wannan gida na gwamnati da zarar sarki ya shiga ya sauka, sai shugabannin ƙananan hukumomin Birni da Tarauni su je su yi gaisuwa ga sarki. Sannan sai gwamna da kansa ya taso ya tarbi sarki sannan su jera su zauna, su yi wa juna barka da salla. Daga nan kuma sai hakimai su gaida sarki.

Bayan sarki ya gama karɓar gaisuwar hakimai, sai kuma Wazirin Kano ya buɗe taro da addu’a. Idan kuma baya nan sai Wali, idan baya nan sai Matawalle. Sai kuma sarki ya yi jawabi sai gwamna ma ya yi nasa jawabin. Sai a rufe taro da addu’a. Sarki ya sake hawa ya fita.

Idan sarki ya fito daga gidan gwamna yana hawa kan Titin Lodge Road, ya bi ta gaban asibitin Nassara wanda a yanzu (2018) ake kira Asibin Abdullahi Wase. Sannan ya gangare zuwa jikin tashar jirgin ƙasa, ya karyaka ya je shatale-talen babban hotel ɗin santara, sannan ya sake karyakawa ya hau titin MTD, sanna ya juya dama ya faɗa Murtala Muhammad Way kamar zai tafi filin jirgin sama. Idan ya zo mararrabar Zainab Galare, sai ya saka gabansa Yamma ya nufi Kasuwar Sabon Gari. Idan ya iso shatale-talen bata; gaban kamfanin Koca-cola, sai ya tasa dama, ya yi Kudu ya hau kan titin Ibo har sai ya zo mararrabar titin Ibo-Faransa, sai ya juya Yamma ya hau kan Titin Faransa ya miƙe ɗoɗar zuwa mararrabar Titin Katsina da Gidan Jaridar Tirayom, sannan ya juya Kudu ya shiga Fagge ta Ƙofar Wafa, ta gana Kasuwar Wafa, ya miƙe Kudu maso Gabas, ya fita ta Ƙofar Abbale da ke kallon kasuwar Kantin Kwari ya yi kamar zai shiga Kasuwar Kantin Kwari sai ya tasa dama ya juya Yamma ya wuce ta Arewa da masallacin idi, ya shiga Ƙofar Mata, ya wuce Karofin Ƙofar Mata har ya kawo Masallacin Gidan Sarki sannan ya sauka.

Idan sarki ya sauka sai hakimai su yi gaisuwa kamar yadda aka saba. Bayan an gama karɓar gaisuwa kuma sai sarki ya shiga gida ta Ƙofar Fatalwa.

Manazarta:


Gwangwazo (2004). Gamzaki mai Asubahi, In Ya fito Gari Ya Waye, Sarkin Kano Alhaji (Dr.) Ado Bayero.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub