Me ka ke nema?


Shafin Farko

Kasuwar BachirawaTukwanen Ƙarfe

Gabatarwa

Kasuwar Bachirawa wacce aka fi sai da ‘yan tukwane, kasuwa ce da ke Bachirawa Kwanar Ungogo kan titin Katsina, a cikin garin Kano, kuma kasuwa ce ta ƙasa-da-ƙasa wacce ake sana’antawa tare kuma da sayar da tukwanen da ake samarwa daga alminiyom. Abin da Bahaushe yake kira da tukunyar ƙarfe.

An kafa wannan kasuwa a shekarar 1990 zamanin shugabancin gwamnan soja Kanal Idris Garba a ƙarƙashin shugabancin Ibrahim Badamasi Babangida. An kafa ta da nufin tsugunnar da ‘yan Kasuwar Sabon Gari masu sana’ar ƙirar tukwanen da nufin sake samar wa su masu sana’ar ƙirar tukunya matsugunin din-din-din tare kuma da sake faɗaɗa harkokin kasuwancin jahar Kano; wato kenan wannan kasuwar kamar wani reshe ce ta Kasuwar Sabon Gari.

Sannu-sannu kasuwar ta buƙansa sakamakon canjin sheƙa da masu irin wannan sana’a suka riƙa yi daga sauran kasuwannin ciki da wajen jahar Kano kamar irin su Kasuwar Ƙofar Ruwa, garuruwan Minjibir, Ɗambatta, Katsina da sauransu.

Kayayyaki

Anna sana’anta kayayyaki da suka haɗa da tukwane masu manya, matsakaita da kuma ƙananan girma. Ana sana’anta tandodin waina, ludaya, cokula, kujerun zama na mata, sassan ababen hawa kamar mota da sauransu. Sannan kuma a wannan kasuwa ana sarrafar sinadaran tagulla, azurfa alminiyom, kwafa-waya, tutiya, da sauransu.


Tandar Ƙarfe

Abokan Hulɗa

Zamowar wannan kasuwa ta ƙasa-da-ƙasa tana hulɗa da garuruwan cikin gida Najeriya da kuma wasu ƙasashen waje. Daga cikin ƙasashen waje akwai China, Indiya, Niger, Burkina Fasso, Chadi da sauransu.

Manazarta:


Tattaunawa da Rafani Sulaiman, shugaban ƙungiyar ‘yan kasuwa a ranar Alhamis 27/12/2018.

Ziyarar gani da ido a ranar Alhamis 27/12/2018.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub