Me ka ke nema?


Shafin Farko

Yaƙin Turawa


A ƙarshen shekarar 1902, zuwa farkon shekarar 1903, Rundunar sojojin Birtaniya ƙarƙashin ƙaura ko barde Morland, wanda kanal ne na soja, ta farmaki ƙasar Kano da yaƙi. Rundunar tana ɗauke da mayaƙan da yawansu ya kai dubu ɗaya da ɗari huɗu da tamanin da biyu, ɗauke da muggan makaman da suka haɗa da atilare, zungureriyar bindiga mai tsawon milmita 75 da kuma wasu bindigu na musamman.

Samun labarin zuwan Turawan ya saka sarkin Kano na zamanin; Alu Maisango ya sake sabunta ganuwa, ƙofofi da kuma gwalalon garin. An ƙara tsayi da kaurin ganuwar da ƙofofi, ta yadda a wasu guraren tsawonta yakan kai kimanin ƙafa hamsin, wasu guraren kuma ƙafa talatin. Shi kuma gwalalon aka ƙara masa faɗi.

Zaton rashin zuwan Turawan ya saka sarkin tafiya garin Sakkwato kai caffa, domin samun karɓuwa a wajen sarkin Musulmi na zamanin wato Sarki Attahiru I. Bayan sarki ya fita daga Kano, sai Turawan suka ɓullo ta garin Bebeji, garin da aka fara gwabza yaƙi da su Turawan, biyowa bayan umarnin da sarkin ya bayar cewa idan suka zo Bebejin a datse su.

Haka nan a garin Kano sarki ya tanadi mayaƙan da ko da Turawan sun zo, za su gwabza da su. Haka kuwa aka yi. Da rundunar mayaƙan Ingila suka iso Kano, sun haɗu da fushin dakarun Kano. Duk wani yunƙuri na shiga garin daga gefen sojojin ya ci tura a karon farko. Sai daga ƙarshe, mayaƙan Birtaniyan suka canja dabara, suka kewaya ta Yamma, suka ɓalla Ƙofar Kabuga, suka shiga ta cikinta.

Faruwar wannan lamari ta saka zaratan mayaƙan birnin na Kano suka dafe hula. Bayan da Turawan suka shiga garin, sai ya koma hannunsu. Duk lokacin aka yi wannan, shi sarki Alu yana kan hanyarsa ta dawowa gida labari ya iske shi a kan hanya cewa Turawa sun ci Kano.

Samun wannan labari ya saka tawagar sarki rabuwa gida biyu; sarki da wasu jama'arsa suka juya zuwa Sakkwato domin bai wa Sarki Attahiru I gudunmawar da za ta kare garin a matsayin cibiyar Daular Usmaniya daga faɗawa hannun Turawa. Ɗaya yankin kuma suka dawowa gida.

A cikin tawagar da ta dawo gida Kano, akwai Muhammadu Abbas, wanda aka naɗa a matsayin sabon sarkin Kano ƙarƙashin mulkin Turawa.

Ita kuma waccar tawaga ta sarki Alu, kafin ta shiga garin Sakkwato sai ta yi kiciɓis da sojojin da suka nufi Sakkwato da yaƙi. Saboda, haka, aka sauya masa hanya zuwa Lokoja domin gudun hijira.

Waɗannan abubuwa da suka faru, su suka tabbatar da karshen mulkin sarki Alu da kuma kawo ƙarshen zaman Kano a ƙarƙashin Daular Shehu da kuma faɗawarta hannun Turawa.

Manazarta:


Abubakar A. Y. (2011). Maitama Sule Ɗanmasanin Kano. Ahmadu Bello Uniɓersity Press, Zaria, Kaduna State, Nigeria.

Audu M. S. da Osuala U. S. (2015). The Biritish Conquest and Resistance of Sokoto Caliphate, 1897 – 1903: Crisis, Conflict and Resistance. Department of History and International Studies, Federal University Lokoja, Kogi State, Nigeria. Historical Research Letter. Vol. 22, 2015, ISSN 2224 – 3178.

Bala A. A. (2015). The Impact of Colonisation in Uprooting Islamic Polity and Introducing Circularism in Northern Nigeria. Department of Islamic Studies, Faculty of Art and Islamic Studies, Usman Ɗanfodiyo University, Sokoto, Nigeria. E-Proceedings on Arabic Studies and Islamic Civilization, iCASIC 2015 (E-ISBN 978-967-0792-02-6), 9 – 10 March 2015, Kuala Lumpur, Malaysia.

NNPC (2007). Hausawa da Maƙwabtansu (2). Northern Nigerian Publishing Company, Gaskiya Building, Zaria, Kaduna State, Nigeria.

Sanusi N. M. (2009). Stories of Dutse Palace, 1421 – 2009. Jigawa State Printing Press, Dutse, Jigawa State, Nigeria.

Rodney W. (1973). How Europe Underdeveloped Africa. Bogle-L ‘Ouverture Publications, London and Tanzanian Publishing House, Dar-Es-Salam.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub