Me ka ke nema?


Shafin Farko

Gwamnan Kano Aliyu Sabo Bakin Zuwo 1983 - 1983Gwamna Sabo Bakin Zuwo.

Gabatarwa

Shi ne gwamnan Kano mafi gajartar zango, ya zauna a wannan kujera na tsawon watanni biyu kawai. Shi mutumin unguwar Bakin Zuwo ne, wanda daga sunan unguwar ne ma ya samu Laƙabinsa na ‘Sabo Bakin Zuwo’. Wannan unguwa tana nan a cikin ƙwaryar birnin Kano. An haife shi a wannan unguwa ta Bakin Zuwo a ranar 31 ga watan Disamba na shekarar 1934.


Karatu

Duk da cewa bai yi nasarar fara karatun zamani tun yana ƙarami ba, ya fara ne da karatun Ƙur’ani a nan unguwar tasu ta Bakin Zuwo. Ya fara karatunsa na Zamani a makarantar Shahuci, inda ya halarci darrusan yamma (Karatun manya na yaƙi da jahilci). Daga baya ya shiga makarantar ‘Ibo (Igbo) Union School’ da ke Sabon Garin Kano. Sannan kuma ya zarce zuwa makarantar mulki ta zariya (Zaria administration Institute).

Muƙaman da ya Riƙe

Ya zama shugaban ƙungiyar ‘yankasuwa (United Labour Congress) reshen jahar Kano. Sannan ya zama mataimakin shugaba, na ƙasa, na wannan ƙungiyar. Ya yi aiki tare da kwamatin tantance masu karɓar bashi na jahar Kano (State’s Rent Assesment Committee). Sannan ya zama shugaban Hukumar Ƙayyade Farashi (Chairman Price Control Board). Sannan ya zama shugaban hukumar tsaftace kamfanoni (Chairman Indutrial Council Safety). Haka nan kuma ya taɓa zama shugaban Ƙungiyar ‘Yan’Dambe ta jahar Kano (State’s Ameteur Boɗing Association).

Zamowarsa Gwamnan Kano

Alhaji Sabo bakin Zuwo ya zama gwamnan jahar Kano ƙarƙashin tutar jama’iyyar PRP, bayan lashe zaɓen da aka gudanar a watan Agusta na shekarar 1983.

Gudunmawarsa

Duk da wannan ƙarancin lokaci da ya yi a kan kujerar gwamna, bai rasa abin ambato da ya bari ba, ya samu nasarar mayar da sinimar falas (Palace Cinema) da ke Unguwarsu ta Bakin Zuwo zuwa asibitin haihuwa (meternity home). Ana kiran wannan asibiti da sunansa.

Manazarta:


Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Government Press, Kano.

Ashiwaju G., Enem U. da Abalogu U. (babu shekarar bugu). Cities of the Savannah, A History of Towns and Cities of the Nigerian Savannah. By Nigerian Magazine.

Barau A.S. (2007). The Great Attractions of Kano. Research and Documentation Directorate, Office of the Eɗecutive Governor, Government House, Kano.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Ɗanyaro M.M. (1997). Kano State 30 Years of Statehood (1967 – 1997).

Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

Gwadabe M.M. (2008). Land, Labour and Taɗation in Kano Native Authority: the Case of Kumbotso District 1903-1953. History Department, Ahmadu Bello University, Zaria.

Gwangwazo M.A. (2003). Tarihin Sarakunan Kano 1805 -2003. Gwangwazo M.A. (2003). Kano Garin Albarka (B), Kudu da Arewa.

Gwangwazo M.A. (2003). Tarihin Kano Kafin Jihadi, Wangarawa sun iso Kano, Littafi na Biyu.

Gwangwazo M.A. (2003). Gani ya Kori Ji, Kano da ƙofofinta Fiye da Shekaru 800. Abba Press Nigeria Limited. Aminu Kano Way, Goron Dutse by Prison Junction. Kano-Nigeria.

Kano State Ministry of Commerce. (2000). Kano State of Nigeria, Centre of Commerce. An buga a Sagagi Press, Kano.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Northern Nigerian Publishing Company Ltd. (1979). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Gaskiya Corporation, Zaria.

Obii-Mbta R.A. (1994). Alhaji Ado Bayero and the Rorayl Court of Kano. Carpricorn 25 Limited. Kano-Nigeria.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Coy, No. 27/32, Beirut Road, Kano.

William-Mbta L. A. O. (2001). The Four King-Makers, King-Making in Kano Kingdom. Published in Nigeria by Capricon, 25 Limited, Kano.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub