Me ka ke nema?


Shafin Farko

Rabi'u Musa Kwankwaso 1999 – 2003/2011-2015Gwamna Rabi'u Musa Kwankwaso

Gabatarwa

Rabi’u Musa Kwankwaso, wanda aka fi sani da Kwankwaso. Tsohon gwamnan jahar Kano ne sannan kuma sanata mai ci. Mutum ne jajirtacce, mai ra’ayin siyasar mazan jiya kamar irin su marigayi Malam Aminu Kano. Rabi’u Musa Kwankwaso Bafillace ne a yare.
Ya yi karatu a fannin fasaha har zuwa matakin digiri na biyu a fannin aikin ruwa. Ya kuma yi aiki da hukumar ruwa ta Kano har tsawon shekaru 17 tun daga 1975 har zuwa 1992. Tun kuma daga 1992 ɗin zuwa yau ya ke cikin harkokin siyasa, abin da ya bashi damar tsayawa takarkarun zaɓuɓɓuka dama tare kuma da samun nasara.

Haihuwa

An haifi Rabi’u Musa a garin Kwankwaso da ke cikin ƙaramar hukumar Madobi a jahar Kano, Najeriya, a ranar 21 ga watan Oktoba na shekarar 1956. Shi ɗa ne ga dagacin garin Kwankwaso, daga baya kuma hakimin Madobi, Majidaɗin Kano, Alhaji Musa Salihu Kwankwaso.

Karatu

 • Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi karatun firamare a garin Madobi da Kuma babbar makarantar firamare ta garin Gwarzo.
 • 1970 – 1972: Makaranta Koyon Sana’a ta Wudil (Wudil Craft School).
 • Makarantar Fasaha ta Kano (Kano  Technical College).
 • Kwalejin Kimiyya ta Kaduna (Kaduna Polytechnci). Inda ya samu shedar karatun difloma ƙarama (ND) da kuma babba (HND).
 • 1982 – 1983: Kwalejin Fasaha Middleseɗ (Middleseɗ Polytechnic) da ke ƙasar Birtaniya. Inda ya samu takardar difloma mai zurfi (Postgraduate Diploma).
 • 1983 – 1985: Jami’ar Fasaha ta Loughborough (Loughborough Uniɓersity of Technology), inda ya samu digiri na biyu (master’s degree) a fannin injiniyancin ruwa (water engineering).

Gogayyar Aiki

Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi aiki na tsawon shekaru goma sha bakwai (1975 – 1992) tare da Hukumar Ruwa (WRECA) ta Kano. Ya riƙe muƙamai da dama a wannan ma’aikata tare kuma da bayar da gagarumar gudunmawa.

Zamowarsa Gwamna

An zaɓi Injiniya Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso a matsayin gwamnan Kano a karo na farko a shekarar 1999 a ƙarƙashin tutar jama’iyyar PDP. An kuma sake zaɓensa a karon an biyu a shekarar 2011 duka a tutar jama’iyyar PDP.

Gudunmawa

Haƙiƙa, kasancewar injiniya dakta Rabi’u Musa Kwankwaso mai aƙidar ganin an raya ƙasa tare kuma da ciyar da mutane gaba, ya bayar da gagarumar gudunmawa. Saboda haka gwargwadon hali a wannan rubutu za mu zayyano abin da ya samu a rukunance; wato fanni-fanni kenan. Abin nufi shi ne cewa za mu bi fanni-fanni na rayuwa mu ga irin gudunmawar da ya bayar:

 1. Fannin Ilimi: Rabi’u Musa Kwankwaso ya baiwa jahar Kano gudunmawa mai gwaɓi a wannan fanni na ilimi. Shi da kansa ya ce, “muna alfahari da abin da muka yi a fannin ilimi…mun gina makarantun sikandire sama da ɗari biyu da talatin. Kuma babban abin farin ciki shi ne cewa guda 44 daga cikinsu makarantun nazarin addinin Musulunci ne. Akwai kuma makarantun koyon sana’a (technical schools) guda 47. Mun ciyar da ɗaliban makarantun firamare tare kuma da raba musu kayan makaranta kyauta, abin da ya haifar da hauhawar yawan ɗaliban na firamare daga miliyan ɗaya kamar yadda muka gada zuwa miliyan uku kamar yadda muka bari…”. Ga wasu kaɗan daga cikin jerin ayyukan Rabi’u Kwankwaso a wannan fanni na ilimi:


  Amana Firmare, Dawakin Kudu L.G.A.

  • Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Wudil: A zangon mulkinsa na farko da ya yi daga 1999 zuwa 2003, ya samar da jami’a kimiyya da fasaha (Uniɓersity of Science and Technology) da ke Wudil.
  • Jami’ar Dakta Yusuf Maitama Sule: A zangon mulkinsa na biyu ya gina jami’ar Arewa-Maso-Yamma (North –West University) wacce aka canjawa suna ta koma (Yusuf Maitama Sule Unviersity).


   Ginin Sanet na Jami'ar North-West

  • Makarantar Kwamfuta ta Kano (Kano Informatics Institute): Wannan makaranata tana nan a garin Kura. An samar da ita a shekarar 2011. Ana yin karatu har zuwa matakin babbar difilomar ƙasa-da-ƙasa (International Diploma) a fannin kwamfuta. Duk wanda ya samu takardar shedar wannan babbar difiloma, yana da damar ci gaba da karatun digiri cikin wasu ƙasashe da suks haɗa da Singapore,  Uganda, da sauransu cikin shekara ɗaya.
  • Makarantar Wasannin Motsa Jiki (Kano Sports Institute) da ke garin Ƙarfi, kan hanyar Zariay.
  • Makarantar Koyon Kiwon Kifi (Kano Fisheries Institute).
  • Makarantar Koyon Kasuwanci da Cinikayya (Kano Entrepreneurship Institute).
  • Makarantar Koyon Aikin Jinya da Ungozoma (Kano Post Basic Midwifery Institute) da ke Gezawa.   
  • Makarantar Koyon Tuƙin Mota (Kano Driɓing Institute).
  • Makarantar Koyon Aikin Tsaro (Kano Corporate Security Training Institute).
  • Makarantar Koyon Noman Rani (Kano Irrigation Training institute).
  • Makarantar Koyon Karatun Alƙur’ani Haɗe da Ilimin Zamani (Kano Institute of Ƙur’anic and Western Education).
  • Makarantar Koyon Aikin Furanni (Kano Horticulture Institute).
  • Makarantar Koyon Kiwon Tsuntsaye (Kano Poultry Institute).
  • Makarantar Koyon Kiwon Dabbobi (Kano Liɓestock Institute).
  • Makarantar Koyon Aikin Na’urorin Noma (Kano Farm Mechanised Institute).
  • Makarantar Haɓɓaka Aikin Jarida (Kano Journalism Deɓelopment Institute).
  • Makarantar Koyon Harkokin Yawon Buɗe-Idanu (Kano Hospitality Management Institute).
  • Makarantar Aikin Fim (Kano Fim Academy).
  • Ginin Makarantun Firamare masu bene hawa ɗaya sama da 150.
  • Gina Makarantun Fasaha (Technical Colleges) 47 duka na kwana.
  • Gina Makarantun nazarin addini Musulunci (School for Islamic Studies) 44 duka kuma na kwana.
  • Tura ɗalibai sama da dubu uku zuwa ƙaro karatu a ƙasashen waje a faɗin duniya.
  • Ɗaukar nauyin ɗalibai a jami’o’in gida Najeriya.
  • Bayar da horon ƙwarewa ga malamai sama da dubu arba’in na makarantun jahar Kano da suka haɗa da firamare, sikandire, da manyan makarantu dan cika sharaɗin samun ƙaramar shedar karantarwa a kowane mataki. A wannan tsari mai takardar shedar sikandire an tura shi ya samo NCE dan karantarwa a firamare, mai digiri ko HND kuma aka tura shi dan samu horo a fannin karantarwa (PGDE), duka kyauta kuma ana gudanar da karatuttukan ne a lokacin hutu sannan kuma a ƙarshen mako.
 2. Fannin Gina Gari da Samar da Muhalli: A wannan fanni ya samar da gidaje masu yawa. Shi ya gina biranen Kwankwasiyya, Amana, da kuma na Bandirawo.


  Birnin Bandirawo

 3. Harkar Sufuri da Zirgazirga: A wannan fanni na sufuri, Tsohon Gwamna Kwankwaso ya gyara tituna, ya yi wasu sababbi, ya rarraba motoci ga matasa dan samar da ayyukan yi. Daga cikin irin ayyukan da ya malama a wannan fanni akwai samar da fitilun kan titi, gina gadonjin sama na mota guda uku, gina hanyoyin ƙasa, da sauransu.
 4. Harakar Lafiya da Kula da Tsaftar Muhalli: Kwankwaso ya gina asibitoci ya kuma inganta wasu. Ya samar da motocin ɗaukar marasa lafiya, da kuma motocin shara.
 5. Kiyaye Haɗɗura da Kashe Gobara: Ya Injiya Kwankwaso ya samar da motocin kashe gobara da sauran kayan aiki ga hukumar kiyaye haɗɗura da kashe gobara ta jahar Kano.

Manazarta:


Barau A.S. (2007). The Great Attractions of Kano. Research and Documentation Directorate, Office of the Eɗecutive Governor, Government House, Kano.

Gwadabe M.M. (2008). Land, Labour and Taɗation in Kano Native Authority: the Case of Kumbotso District 1903-1953. History Department, Ahmadu Bello University, Zaria.

Kano State Ministry of Commerce. (2000). Kano State of Nigeria, Centre of Commerce. An buga a Sagagi Press, Kano.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub