Me ka ke nema?


Shafin Farko

Gwamnan Kano Dominic Obukadata Oneya 1996 - 1998Dominic Oneya

Gabatarwa

Kanal D.O. Oneya, shi ne gwamnan Kano na goma sha uku. An haife shi a a ranar 26 ga watan Mayu na shekarar 1948 (24 May, 1948) a garin Agrarho da ke Ƙaramar hukumar Ughelli ta Arewa, a jahar Delta.

Karatu

A makarantar firmare ta Baptist da ke Apapan Legas ya yi karatunsa na firmare daga shekarar 1954 zuwa 1961. Daga nan ya tsallaka zuwa makarantar sikandire ita ma ta Baptist ɗin ita kuma a Yaba duk a Legas, daga shekarar 1962 zuwa 1966. A jami’ar Obafemi Awolowo da ke Ile-Ife ya samu karatunsa na digirin farko a fannin ‘Physical Education’.

Bayan kammala karatunsa na digiri, kamar yadda aka saba ya fara aiki sannan kuma ya ci gaba da halartar kwasakwasan da ke ƙara masa sanin makamar aiki. Ya kuma shiga makarantar sojoji da ke (NDA) ta Kaduna (Nigerian Defence Academy, Kaduna) a ranar shida ga watan Mayu na shekarar 1969. Ya halarci kwasakwasai da dama, daga ciki akwai waɗanda ya yi a Nijeriya da kuma Ghana sannan kuma sai Kanada (Canada), duk a fanninsa na soja.

Shigarsa Soja

A watan Satumba na shekarar 1971 ya samu shiga rundunar sojan Nijeriya a fannin ‘Infantry’. Ya yi aiki tare da rundunar soja ta 31 daga 1971 zuwa 1972.

Gogayyar Aiki

Ya zama malamin makaranta a ‘Division Training Scholl – 4 Division’, daga 1972 zuwa 1973. Daga nan aka mayar da shi mai tsaron lafiyar shugaban sojoji (ADC to the chief of army staff) Janar David Ejoor, daga shekarar 1974 zuwa 1975, sannan kuma ya koma Jaji a matsayin malamin makaranta a ‘Nigerian Military Training College’ daga 1975 zuwa 1977. Daga nan kuma aka tura shi ƙasar Labanan ya yi aki tare da rundunar sojan Majalisar Ɗinkin Duniya (United Nations Forces) a matsayin ofisa ofareshin, daga shekarar 1980 zuwa 1981. Sannan ya taɓa zama shugaban ma’aikatan helikwatar sojoji mai daraja ta biyu (Staff Officer Grade II Nigerian Army Headƙuaters, Lagos) da ke Legas a shekarar 1982 zuwa 1984.

Ya zama kwamadan makarantar sojojin Nijeriya da ke Zariya (Commandant, Nigerian Army Physical Training School, Zaria), daga shekarar 1985 zuwa 1987. Sannan kuma ya juya zuwa makarantar sojoji ta Jaji a matsayin daraktan ma’aikata na wannan makaranta, daga shekarar 1988 zuwa 1989. Daga nan kuma sai aka ƙetara da shi Gana ya zama daraktan ma’aikata a nan ma na kwalejin sojojin Gana da ke Teshi a Akara ta ƙasar Gana (Directing Staff, Ghana Armed Forces Staff College, Teshie, Accra, Ghana) daga shekarar 1989 zuwa 1991.

Daga shekarar 1991 zuwa 1992 ya riƙe bataliyar sojojin Najeriya ta 82 da ke Katsina a matsayin kwamanda.  Daka baya kuma ya zama kwamandan riƙon ƙwarya na rudunar sojan Najeriya ta 3 da ke Kano.

Shi ya jagorancin bataliyar sojojin Nijeriya ta 16 zuwa ƙasar Laberiya. Daga shekarar 1993 zuwa 1995.  Bayan dawowarsa ne daga Laberiya aka yi masa darakta mulki da tsaretsare na helikwatar horon sojojin Nijeriya da ke Minna ta jahar Neja (Director Admnistration and Logistics, Headƙuaters Training and Doctrine Command, Nigerian Army, Minna) daga shekarar 1995 zuwa 1996.

Zamowarsa Gwamnan Kano

Kanal D.O. Oneya, ya zama gwamnan Kano wata Agusta na shekarar 1996. Wannan naɗi nasa ya fara aiki a ranar 23 ta watan Agusta ɗin shekarar 1996.

Gudunmawar da ya Bayar

Tabbas, mutum mai tarin gogayya kamar Kanal D.O.Oneya, ba zai rasa rawar takawa ba a kan wannan muƙamin nasa na gwamna. Ya bayar da gudunmawarsa gwargwadon iyawa dan kawo ci gaba a Kano.

Daga cikin ayyukan da gwamna Oneya ya yi a Kano akwai samar da kayayyakin karatu a makarantun firmare da sikandire na jahar Kano, raba taraktocin noma guda hamsin da injinan casa, sussuka da sauransu. Sabunta asibitoci da gina wasu, samar da maguguna a asibitoci, gina rijiyoyin birtsatse. Da sauran ayyuka masu tarin yawa.

Manazata:


Barau A.S. (2007). The Great Attractions of Kano. Research and Documentation Directorate, Office of the Eɗecutive Governor, Government House, Kano.

Gwadabe M.M. (2008). Land, Labour and Taɗation in Kano Native Authority: the Case of Kumbotso District 1903-1953. History Department, Ahmadu Bello University, Zaria.

Gwangwazo M.A. (2003). Tarihin Sarakunan Kano 1805 -2003. Gwangwazo M.A. (2003). Kano Garin Albarka (B), Kudu da Arewa.

Gwangwazo M.A. (2003). Tarihin Kano Kafin Jihadi, Wangarawa sun iso Kano, Littafi na Biyu.

Gwangwazo M.A. (2003). Gani ya Kori Ji, Kano da Ƙofofinta Fiye da Shekaru 800. Abba Press Nigeria Limited. Aminu Kano Way, Goron Dutse by Prison Junction. Kano-Nigeria.

Kano State Ministry of Commerce. (2000). Kano State of Nigeria, Centre of Commerce. An buga a Sagagi Press, Kano.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub