Me ka ke nema?


Shafin Farko

Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi 1979 – 1983Gwamna Abdu Baƙo.

Gabatarwa

Shi ne zaɓaɓɓen gwamnan Jahar Kano na farko. An zaɓe shi a jamhuriyya ta biyu ƙarƙashin tutar jama’iyyar PRP wacce ke da ma’ana ta (People Redemption Party). Shi mutumin garin Rimi ne da ke cikin gundumar Sumaila (wacce yanzu ta zama ƙaramar hukumar Sumaila) ta ƙaramar hukumar Wudil a cikin jahar Kano. An haife shi a shekarar 1940.

Karatu

Ya fara karatunsa na firamare a garin Sumaila a ƙaramar firamare (junior primary school) daga shekarar 1950 zuwa 1956.  Daga nan ya samu wucewa zuwa babbar makarantar firamare (senior primary school) da ke Birnin Kudun jahar Kano wacce yanzu ta ke cikin Jahar Jigawa, daga shekarar 1956 zuwa 1958. Sannan kuma daga shekarar 1959 zuwa 1960 ya halarci makarantar (Clerical Training Centre) da ke Sakkwato. Daga nan ya samu nasarar tafiya makarantar koyon mulki (Institute of Administration, Zaria) da ke Zariya a shekarar 1961.

1974, ita ce shekarar da marigayi Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi ya samu nasarar shiga Jami’ar Landan (university of London), inda ya karanta dangantakar ƙasa-da-ƙasa (International Relations) a matsayin difiloma (Diploma), karatun da ya bashi nasarar zarcewa zuwa digiri na biyu, duka dai a cikin wannan shekarar. Ya samu wannan karatu nasa ne a Jami’ar Susek (University of Sussex ), duka dai a Landan ɗin. A wannan makaranta mai dangantakar ƙasa-da-ƙasa ya yi karantu. Ya kammala wannan karatu nasa a shekara 1975, inda ya fita da ‘Masters of Arts Degree’.

Gogayyar Aiki

Tun farkon kammala karatunsa da ya yi a Zariya a fannin mulki, ya koma makarantarsa ta Sakkwato inda ya zama malami a can, a cikin shekarar 1962 zuwa 1964. Daga nan kuma sai ya koma Ƙaramar Hukumar Birni (Kano Local Government), inda ya yi aiki a fannin ajiya (treasury) na ƙaramar hukumar. Ya yi aiki a wannan guri tun daga shekarar 1965 har zuwa 1966. Ya bar wannan ma’aikata ya canja sheƙa zuwa Ma’aikatar Yaɗa Labarai ta Gwamnatin Tarayyar Najeriya da ke Legas (Federal Ministry of Information, Lagos). Ya yi aikinsa ne a matsayin jami’in yaɗa labarai (Information Officer) daga shekarar 1966 zuwa 1970.

A shekarar 1970 aka tura shi ya zama jami’in yaɗa labarai da al’adu a ofishin jakadancin Najeriya da ke ƙasar Masar (Nigerian Embassy, Cairo). Ya yi aiki a wannan gurin tun daga 1970 har zuwa 1972. Ya yi aiki da Makarantar Harkokin Ƙasa-da-ƙasa ta Najeriya da ke Legas (Nigerian Institute of International Affairs, Lagos) a shekarar 1976 har zuwa 1977, muƙamin magatakarda a fannin mulki (Administrative Secretary) ya riƙe a wannan makarantar.

An zaɓe shi ya zama mamba a majalisar mazaɓu (Constituent Assembly) mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Gwarzo, wacce ta haɗe ƙananan hukumomin Gwarzo da Ƙaraye. An zaɓe shi a matsayin mataimakin magatakardar jama’iyyar PRP na ƙasa (Deputy National Secretary) a Disambar 1978 (December, 1978). Bayan wata shida da wannan zaɓe aka tsayar da shi ɗantakarar gwamnan Kano, ƙarƙashin jama’iyyar PRP. An yi wannan a ranar 25 ga watan Yuni na shekarar 1979 (25 June, 1979).

Zamowarsa Gwamnan Kano

Zaɓen da aka gudanar a ranar 28 ga watan Yuli na shekarar 1979 (28 July, 1979), shi ya tabbatar da shi a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan jahar Kano na farko, kuma gwamna na huɗu a jahar. An rantsar da shi a matsayin gwamna a ranar 1 ga watan Oktoba na shekarar 1979 (1 October, 1979).

Gudunmawarsa

Haƙiƙa, marigayi Muhammadu Abubakar Rimi, ya bayar da gudunmawa mai gwaɓi wajen bunƙasar jahar Kano, birni da ƙauyuka. Kusan ma ana iya cewa abu ne mai wahala a iya ƙididdige ci gaban da ya kawo jahar Kano. Amma ana iya ɗan gutsuro wasu muhimmai.

A shekarar da ya hau mulki, 1979, ya fara da soke karɓar haraji da jangali da ake yi a hannun jama’a, sannan kuma ya kafa ma’aikatar ci gaban karkara da birane (Ministry of Rural and Community Development).

A cikin shekarar 1980, ya shelanta ranar ɗaya ga watan Mayu ta zama ranar ma’aikata, saboda gudunmawa da su ma’aikatan ke bayarwa wajen ci gaba a kowanne fanni. Wannan abu da ya yi daga baya gwamnatin tarayyar Nijeriya ta mai da shi ya zama ɗaya daga cikin ranakun hutun da take bayarwa har yau ɗin nan.

Sannan shi ya ƙirƙiri hukumar nan ta ilimin manya (Agency for Mass Education), hukumar da ta samu yabon ƙasashen waje saboda gagarumar gudunmawar da ta bayar wajen ilimantar da mutane. Shi ya kafa gidan jaridar Tirayomf (Triumph Publishing Company) da kuma gidan Talabijin na 'CTV 67', wanda daga baya aka mayar da shi 'ARTƁ' mai ma’ana ta 'Abubakar Rimi Television' bayan rasuwa dan tunawa da sunansa.

Muhimman Ayyukan da Marigayi Muhammadu Abubakar Rimi ya malala sun haɗa da kafa hukumar hasken wutar lantarki ta karkara wacce aka ɗorawa alhakin ganin ta haskaka karkaru da wutar lantarki. Ruwan sha, asibitoci, hanyoyi, da makarantun sikandire na daga cikin ababen da marigayi Gwamna Rimi ya samar a iya faɗin jahar Kano.

Hakanan a yunƙurinsa na kusanta gwamnati da jama’a da kuma kusanto da jama’a zuwa ga gwamnati ya ƙirƙiri masarautu guda huɗu da suka haɗa da Gaya, Dutse, Rano da Auyo. Sannan kuma ya ƙirƙiri ƙananan hukumomi guda tara, ƙanan hukumomin da gwamnatin sojan da ta hamɓarar da jamhuriya ta biyu ta ruguje su.

Shi fara aikin makarantar koyon aikin jinya (Kano School of Nursing). Haka nan shi ya samar da hukumomin kula da aikin gona na KNARDA da kuma KASCO tare da tallafin Bankin Duniya. Daga cikin ayyukan da ya tafi ya bari akwai gina katafariyar cibiyar zuba jari ta Kano (Kano Investment House) wanda a yanzu Jami’ar Northwest ke gudanar da hulɗoɗinta a gurin. Akwai kuma ginin kasuwar duniya da ya fara (Kano State Trade Fair) wacce ke kan titin gidan zu.

A yunƙurinsa na inganta yawon shaƙatawa da buɗe idanu ya gina hotel ɗin Magwan. Da sauran muhimman ayyuka. Wani tarihi da marigayi Muhammadu Abubakar Rimi ya kafa a siyar Nijeriya shi ne na sauka daga kan kujerarsa ta gwamna dan sake tsayawa zaɓe a karo na biyu.

Manazarta:


Barau A.S. (2007). The Great Attractions of Kano. Research and Documentation Directorate, Office of the Eɗecutive Governor, Government House, Kano.

Gwadabe M.M. (2008). Land, Labour and Taɗation in Kano Native Authority: the Case of Kumbotso District 1903-1953. History Department, Ahmadu Bello University, Zaria.

Gwangwazo M.A. (2003). Tarihin Sarakunan Kano 1805 -2003. Gwangwazo M.A. (2003). Kano Garin Albarka (B), Kudu da Arewa.

Gwangwazo M.A. (2003). Tarihin Kano Kafin Jihadi, Wangarawa sun iso Kano, Littafi na Biyu.

Gwangwazo M.A. (2003). Gani ya Kori Ji, Kano da Ƙofofinta Fiye da Shekaru 800. Abba Press Nigeria Limited. Aminu Kano Way, Goron Dutse by Prison Junction. Kano-Nigeria.

Kano State Ministry of Commerce. (2000). Kano State of Nigeria, Centre of Commerce. An buga a Sagagi Press, Kano.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub