Me ka ke nema?


Shafin Farko

Gwamnan Kano Sani Bello 1975 – 1978Gwamna Abdu Baƙo.

Gabatarwa

Kanal Sani Bello shi ne gwamnan jahar Kano na biyu. Shi mutumin Kwantagora ne wacce ke cikin jahar Neja a yau. An haife shi a garin Kwantagora a ranar 27 ga watan Nuwamba na shekarar 1942 (27 November, 1974). Sunan mahaifinsa Alhaji Bello Mustapha. Mahaifiyarsa kuma sunanta Hajiya Abu.

Karatu

Ya yi karatunsa na firamare a makarantar fimare ta Kwantagora (Kontagora Primary School) daga shekarar 1950 zuwa 1956. Bayan kammala karatunsa na firamare ya samu nasarar shiga makarantar gaba da firamare mai suna (Provincial Secondary School Bida) da ke Bida wacce yanzu ta koma (Government College, Bida), daga shekarar 1957 zuwa 1962.

Shigarsa Aikin Soja

Ya shiga aikin soja a shekarar 1962 inda ya halarci makarantar horas da sojojin Najeriya da ke Kaduna (Nigerian Military Training College, Kaduna). Ya samu zuwa ƙarin horo a makarantar sojoji da ke Sandhurst (Royal Military Academy, Sandhurst) daga 1963 zuwa 1965.

Muƙaman da ya Riƙe

Bayan dawowarsa aka turashi zuwa bataliyar sojoji da ke Inugu inda ya bada gudumawa a fannonin soja dabam-dabam. Ya jagoranci rundunoni soja da dama. A lokacin yaƙin basasa, ya riƙe muƙamin kwamanda mai taken (Bonny Sector Commandor). Bayan ƙare yaƙin kuma aka tura shi Legas a matsayin shugaban ma’aikatan ‘Lagos Garrison Organization’. Sannan ya riƙe muƙamin kwamandan cibiyar ‘Oshodi Resettlement Center’ da ke Oshodin Legas. Ya riƙe muƙamai da dama a gidan soja kafin zamowarsa gwamnan Kano. Matakin ƙarshe da ya taka kafin zamowarsa gwamnan Kano shi ne zamowarsa kwamadan bataliya ta tamanin da ɗaya da ke Kaduna (Commanding Officer 81 Batallion, Kaduna).

Gudunmawa

Gwamnatin Kanar Sani Bello ta bayar da gagarumar gudunmawa wajen ci gaban jahar Kano. Ya bayar da muhimmiyar kulawa wajen harkar ilimi. Daga cikin muhimman gudunmawoyin da ya bayar akwai kafa hukumar kula da makarantun kimiyya (Science Secondary Schools Management Board), a ƙarƙashin wannan hukuma aka ƙirƙiri makarantar kimiyya ta Dawakin Kudu (Dawakin Kudu Science Secondary School) da kuma takwararta ta Dawakin Tofa duka a shekarar 1979. Makarantar da ta yaye manyan likitoci da masana harkar lafiya. Babban misali shi ne Sarki Abba Abdulƙadir.

Haka nan ma babbar makarantar ilimi ta ‘Kano State Institute for Higher Education’ a lokacinsa aka yi ta. Daga cikin irin ayyukan da ya malala akwai tabbatar da kafuwar ƙananan hukumomi ishirin waɗanda ya ƙirƙira da tsohon salon mulkin da ake amfani da shin a shiyya-shiyya, sakamakon dokar ƙananan hukumomi da gwamnatin tarayya ta samar.

Kuma dai gwamna Sani Bello shi ya kafa kwamatin jaha na asusun gwamnatin Kano (state public account committee), kwamatin da ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen tsaftace harkar kuɗi a gwamnatin Kano. Ya bar gidan gwamnatin Kano a ranar 30 ga watan Satumba na shekarar 1978 (30 September, 1978).

Manazarta:


Barau A.S. (2007). The Great Attractions of Kano. Research and Documentation Directorate, Office of the Executive Governor, Government House, Kano.

Danyaro M.M. (1997). Kano State 30 Years of Statehood (1967 – 1997).

Gwadabe M.M. (2008). Land, Labour and Taxation in Kano Native Authority: the Case of Kumbotso District 1903-1953. History Department, Ahmadu Bello University, Zaria.

Kano State Ministry of Commerce. (2000). Kano State of Nigeria, Centre of Commerce. An buga a Sagagi Press, Kano.

Yakasai T. (2004). Tank Yakasai, The Story of a Humble Life, An Autobiography, Volume I. Goverment Printers, Kano-Nig


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub