Shafin Farko

Kasuwar 'Yankaba, Kano



Wani Yanki Na Kasuwa 'Yankaba

Gabatarwa

Kasuwar 'yankaba, tana daga cikin kasuwannin ƙasa-da-ƙasa da ke cikin garin Kano a Najeriya. Kasuwa ce ta hadar hadar kayan miyan da sauran kayayyakin abinci da na shayi.

An kafa wannan kasuwa a shekarar 1985. Wannan kasuwa an kafa ta ne da nufin rage cunkoso aKasuwar Sabon Gari. Wannan kasuwa katafariyar kasuwar kayan gwari ce (Kayan gwari su ne ɗanyun kaya da ke lalacewa da wuri kamar irin su tumatir, albasa, ganyayyaki, da sauransu). Kusan a kowace rana akan yi wa motoci lodi daga wannan kasuwa zuwa wasu biranen Ƙasar Nijeriya da ma zuwa ƙasashen ƙetare.

Haja

Babu wata haja da ake kasawa a wannan kasuwa ta 'Yankada da suka wuce ɗanyun kaya abin da a Hausance ake kira kayan gwari ko kuma kayan miya da suka haɗa da timatir, tattasai, albasa, barkono da saurnsu. Haka nan kuma ana samun irin su da kuma busassunsu.


Wani Yanki Na Kasuwa 'Yankaba

Abokan hulɗa

Wannan kasuwa tana mu'amala da ƙasashe da dama, daga ciki akwai: Kamaru, Ghana, Chadi da kuma Nijar.

Kasuwar 'Yankaba ta nan a kan titin Haɗeja a garin Kano.

Manazarta


Barau A.S. (2007). The Great Attractions of Kano. Research and Documentation Directorate, Office of the Executive Governor, Government House, Kano.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Ɗanyaro M.M. (1997). Kano State 30 Years of Statehood (1967 – 1997).

Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

Gwadabe M. M. (2008). Land, Labour and Taxation in Kano Native Authority: the Case of Kumbotso District 1903-1953. History Department, Ahmadu Bello University, Zaria.

Gwangwazo M.A. (2003). Tarihin Sarakunan Kano 1805 -2003. Gwangwazo M.A. (2003). Kano Garin Albarka (B), Kudu da Arewa.

Gwangwazo M.A. (2003). Tarihin Kano Kafin Jihadi, Wangarawa sun iso Kano, Littafi na Biyu.

Gwangwazo M.A. (2003). Gani ya Kori Ji, Kano da ƙofofinta Fiye da Shekaru 800. Abba Press Nigeria Limited. Aminu Kano Way, Goron Dutse by Prison Junction. Kano-Nigeria.

Kano State Ministry of Commerce. (2000). Kano State of Nigeria, Centre of Commerce. An buga a Sagagi Press, Kano.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Northern Nigerian Publishing Company Ltd. (1979). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Gaskiya Corporation, Zaria.

Obii-Mbta R.A. (1994). Alhaji Ado Bayero and the Rorayl Court of Kano. Carpricorn 25 Limited. Kano-Nigeria.

Tattaunawa da Musa Abdulƙadir Zawachiki, sakataren kuɗi na ƙungiyar kasuwar ‘Yan Kaba a ranar 24/12/2018 a ramfarsa da ke kasuwar.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Coy, No. 27/32, Beirut Road, Kano.

William-Mbta L. A. O. (2001). The Four King-Makers, King-Making in Kano Kingdom. Published in Nigeria by Capricon, 25 Limited, Kano.