Shafin Farko

Kasuwar Kurmi


Gabatarwa

Kasuwar kurmi, kasuwar ƙasa-da-ƙasa (Wato duniya) ce a Kano. Ita ce kasuwa mafi daɗewa a ƙwaryar birnin Kano da ma kewayenta. Kusan ana iya cewa ita ta haifar da dukkanin kasuwanin Kano. Abu ne mai matuƙar wahala a iya iyakance lokacin da aka fara cinikayya a wannan kasuwa. A cikin tattaunawar da muka yi da Sarkin Kasuwar Kurmi Alhaji Abdullahi Maikano a ofishinsa da ke cikin kasuwar, ya shaida mana cewa wannan kasuwa ta kafu ne sanadiyyar kwari ko kuma kurmin Jakara wanda masunta da mafarauta suke zuwa suna gudanar da sana'o'insu mabuƙata nama da kuma kifin da suke kamawa suna zuwa su basu wani kayan su kuma su karɓi nasu. Kuma wannan zancen abin tabbatarwa ne daga tarihin yadda garin Kano ya kafu, musamman abin da ya shafi dalilin da ya kawo Bagauda Kano a matsayin sarki. Duba tarihin Kano.

Ginin Kasuwa

Sarkin Kano Muhammadu Rumfa ne ya fara kafa rumfuna a wannan kasuwa tare kuma da fara karɓar haraji (Ƙwalli, 1996; tattaunawa da Sarkin Kasuwa, 2019).

Sarkin Kano Abdullahi Bayero (1926 – 1953), shi ya sabunta kasuwar ya zamanantar da ita. Ya yi mata tashar jakuna; wannan tashar jakuna yanzu babu ita sai dai gurbinta da aka gina masallacin da ake kira Masallacin Shabbabu a gurin. Ita kuwa tashar jakai kewaye ne aka yi wanda duk mutumin da ya kawo kayansa a jaki yakan tafi wannan tasha ya ɗaure jakinsa har zuwa lokacin da zai gama cin kasuwarsa ko kuma ya sayi abin da ya kawo shi. Akwai rijiyoyi da aka tottona a cikin wannan tasha domin shayar da jakuna.

Bayan wannan kuma ya gina rumfunan kasuwa na zamani, kotu, ofishin 'yan sanda, pas-ofis da sauransu. Haka nan ma kuma ya gina tashar mota da aka fi sani da tashar Jakara duk domin wannan kasuwa da kuma walwalar 'yan kasuwa.


Rumfar Kasuwar Kurmi. An gina ta sama da shekaru tamanin da suka shuɗe

Kasuwar tana nan a tsakiyar birnin Kano. Akwai unguwanni da suke zagaye da ita kamar irin su Jakara, Bakin Zuwo, Kwanar Goda, Ƙofar Wambai, da sauransu. Dukkan waɗannan Unguwanni ana kiransu da Bakin Kasuwa a Dunƙule.

Haƙiƙa wannan kasuwa ta bada muhimmiyar gudunmawa wajen cigaban Kano ta fuskacin tattalin arziƙi da kuma ƙaruwar jama’a. Saboda a kodawane lokaci akan samu waɗanda za su zo da nufin kasuwanci amma sai su yi ‘Zuwan Sojan Badaskare’.

Duk da cewa wannan kasuwa har yanzu tana da rumfuna irin na da, to amma tana da zubi mai kyau, sannan kuma a tsare take daki-daki. Misali, akwai rukuni guda na masu sayar da littattafai ne kawai zalla da ake kira ‘yan littattafai. Akwai kuma layi guda na masu sayar da kayan adon dawaki, akwai layin masu sayar da turare. Akwai kayayyakin da ake shigowa da su kamar irin su turare, da ma wasu irin kayayyakin mutanen Nijar. Sannan kuma za ka ga namu na gargajiya.

A zamanin Turawa an yi wa wannan kasuwa gyaran fuska daga asalin yadda take. Sannan kuma kamar idan ka zo bakin hanya akwai gini irin na zamani. Musamman ‘yan littattafa.

Kayayyakin da Ake Sayarwa

Kusan a dunƙule ana iya cewa da wuya ka nemi wani abin masarufi a wannan kasuwa ka rasa, amma duk da haka kasuwa ce da ta shahara wajen sayar da kayayyakin gargajiya da suka haɗa da saƙe da ake yi wa laƙabi da farin Kano; kayan adon dawaki, kayan yaji ko kuma kayan ƙamshi da suka haɗa da citta, kananfari, masoro, da sauransu; suturar gargajiya da suka haɗa da manyan riguna, alkyabba, wundiya da sauransu; kayan yaƙi da suka haɗa da takubba, sulke da saurnasu; kayan ado na fata da suka haɗa da matashi, hula, jaka da sauransu; sinadarin haɗa turarern wuta da na ruwa da sauransu; kayan adon mata da suka haɗa da yari, tsakiya, murjani, dutsen wuya da sauransu; madubi, tozali da sauransu; sai kuma litattafai waɗanda kana iya cewa kusan yanzu su ne ma mafi rinjaye a hajar kasuwar; akwai kuma kayayyaki irin su goriba, ɗinya, kanya, zogale, da sauransu; sannan kuma akwai kayan ƙere-ƙeren gargajiya irin su fartanya, murhu, wuƙa, da sauransu.


Rumfar sayar da citta a Kasuwar Kurmi Kano

Abokan Hulɗa

Kasuwar Kurmi kasuwa ce ta duniya. Daga wannan kasuwa akwai cuɗanyar cinkayya da kusan dukkan ƙasashen Afirka. Kaɗan daga ciki akwai Ghana, Burkina Faso, Nijar, Mali, Sudan, Libiya, Kamaru, Chadi da sauransu.

Manazarta:


Barau A.S. (2007). The Great Attractions of Kano. Research and Documentation Directorate, Office of the Executive Governor, Government House, Kano.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Ɗanyaro M.M. (1997). Kano State 30 Years of Statehood (1967 – 1997).

Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

Gwadabe M.M. (2008). Land, Labour and Taɗation in Kano Natiɓe Authority: the Case of Kumbotso District 1903-1953. History Department, Ahmadu Bello University, Zaria.

Gwangwazo M.A. (2003). Tarihin Sarakunan Kano 1805 -2003. Gwangwazo M.A. (2003). Kano Garin Albarka (B), Kudu da Arewa.

Gwangwazo M.A. (2003). Tarihin Kano Kafin Jihadi, Wangarawa sun iso Kano, Littafi na Biyu.

Gwangwazo M.A. (2003). Gani ya Kori Ji, Kano da ƙofofinta Fiye da Shekaru 800. Abba Press Nigeria Limited. Aminu Kano Way, Goron Dutse by Prison Junction. Kano-Nigeria.

Kano State Ministry of Commerce. (2000). Kano State of Nigeria, Centre of Commerce. An buga a Sagagi Press, Kano.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Northern Nigerian Publishing Company Ltd. (1979). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Gaskiya Corporation, Zaria.

Obii-Mbta R.A. (1994). Alhaji Ado Bayero and the Rorayl Court of Kano. Carpricorn 25 Limited. Kano-Nigeria.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Coy, No. 27/32, Beirut Road, Kano.

William-Mbta L. A. O. (2001). The Four King-Makers, King-Making in Kano Kingdom. Published in Nigeria by Capricon, 25 Limited, Kano.